Kitimurmura: An Bankado Bidiyon Jami’in Hisbah Yana Tallata ’Yancin Alakar Jinsi

Kitimurmura: An Bankado Bidiyon Jami’in Hisbah Yana Tallata ’Yancin Alakar Jinsi

  • Wani bidiyo ya bulla a shafukan sada zumunta wanda ke nuna wani jami'in hukumar Hisbah a Kano yana goyon bayan masu auren jinsi
  • A cikin bidiyon, an ga Idris Ahmed, wanda shugaban sashen kiwon lafiya ne na Hisbah yana adawa da wariyar da ake nunawa 'yan madigo
  • Sai dai shugaban Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa, ya fito shi ma a bidiyo ya nesanta hukumar da kalaman Idris tare da daukar mataki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Shugaban sashen kiwon lafiya na hukumar Hisbah Kano, Idris Ahmed Gama, ya fito a bidiyo yana rajin kare 'yancin masu auren jinsi.

Idris Ahmed ya bayyana matsayarsa kan kungiyar masu rajin kare 'yancin 'yan madigo, auren jinsi, sauya jinsi, 'yan luwadi (LGBTQ) a wata gayyata da wata kungiya ta yi masa.

Kara karanta wannan

"Ban san meye LGBTQ ba": Jami'in Hisbah ya magantu bayan kama shi da tallata auren jinsi

Jami'in Hisbah a Kano ya nuna goyon bayansa ga auren jinsi
Kano: Jami'in Hisbah ya nemi a rusa dokar da ta haramta auren jinsi a Najeriya. Hoto: @el_uthmaan/X, alvaro gonzalez/Getty Images
Asali: UGC

Jami'in Hisbah na rajin kare 'yan madigo

Kamar yadda wani @el_uthmaan ya wallafa bidiyon tattaunawar da aka yi da jami'in na Hisbah a shafinsa na X, Idris Ahmed ya ce 'yan madigo mutane ne kamar kowa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idris Ahmed ya ce:

"Lokacin farko da aka fara gayyata ta zuwa taron da ya shafi masu auren jinsi (LGBTQ) a Abuja, na ji tsoro sosai, ban samu damar sakewa ba gaskiya.
"Amma yanzu da yake shi ne karo na na biyu, bana jin komai. Domin na samu kusanci da 'yan kungiyar LGBTQ, kuma na kara fahimtar cewa su ma mutane ne kamar kowa.
"Babbar matsalar ita ce, nuna wariya da aka yi gare su, wanda ba dai dai bane. Dole ne a daina nuna wariya ga 'yan LGBTQ."

"A sabunta dokar auren jinsi" - Idris

Jami'in hukumar ta Hisbah ya ce akwai bukatar majalisar Najeriya da ta waiwayi dokar da ta haramta auren jinsi a kasar domin a sabunta ta.

Kara karanta wannan

Auren Jinsi: Hisbah ta magantu kan jami'inta da ya bayyana a bidiyon 'wise initiative'

"Mu duka 'yan Najeriya ne, akwai bukatar a ba kowa damar yin rayuwa ba tare da an nuna ma wani wariya ba. Don haka ina fatan 'yan majalisunmu za su waiwayi dokar haramta auren jinsi."

Kalli bidiyon a kasa:

Idris ma'aikacin hukumar Hisbah ne?

Mun tuntubi jami'in hulda da jama'a na hukumar Hisbah ta Kano, Lawal Ibrahim kan ko Idris Ahmed da gaske ma'aikacin hukumar ne.

Lawal Ibrahim ya tabbatar da cewa Idris ma'aikacin hukumar ne, kuma kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Daurawa ya fitar da matakin da aka dauka kan jami'in.

Hisbah ta dauki mataki kan Idris

Bayan fitar wannan bidiyo na Idris Ahmed, shugaban hukumar Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya nesanta hukumar daga kalaman jami'in.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Daurawa ya ce ba hukumar ce ta tura Idris inda ya je ya yi kalaman ba, ya je ne a karan kansa, don haka bai kamata ya alakanta zuwansa da hukumar ba.

Kara karanta wannan

Auren jinsi: Yadda kururuwar mutanen Kano ya dakile yunkurin kungiyar LGBTQ

Shugaban hukumar ya ce yanzu haka an tura Idris zuwa ga sashen dokokin hukumar Hisbah domin a bincike shi tare da gurfanar da shi gaban kotu.

Akwai auren jinsi a yarjejeniyar Samoa?

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ce babu wani lamunin $150bn ko kuma amincewa da auren jinsi a cikin yarjejeniyar Samoa.

Gwamnatin ta ce yarjejeniyar Samoa hadin gwiwa ce tsakanin tarayyar Turai da kasashen Afirka, Caribbean da Pasifik, wadda za ta bunkasa zamantakewa da tattalin arziki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.