Matashi Ya Sassara Tsohuwa Mai Shekaru 60 da Makami, Ya Kasheta Har Lahira
- Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta yi nasarar cafke wani matashi mai suna Adamu Alhassan da ake zargi da kisan gilla wa wata tsohuwa
- Ana zargin Adamu Alhassan da haurawa dakin matar da kuma sara mata makami wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta
- Rundunar yan sanda ta bayyana dalilan da suka sa take zargin Adamu Alhassan da aikata kisan da kuma matakin da ta dauka a kansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi- Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta yi nasar cafke wanda ake zargi da kisan wata tsohuwa.
An kashe tsohuwar ne mai suna Safiya Yunusa a dakinta inda aka ji mata raunuka bayan an sassara ta da makami.
Legit ta tatttaro bayanan ne cikin wani sako da rundunar yan sandan jihar Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bauchi: An kashe tsohuwa mai shekaru 60
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa wani matashi mai suna Aliyu Yunusa ya kai karar cewa an kai hari ga mahaifiyarsa a jiya Lahadi.
Biyo bayan haka ne yan sanda suka isa gidan domin tabbatar da labarin kuma sun samu matar an ji mata rauni da makami a sassan jikinta.
Daga nan ne jami'an tsaro suka nufi asibiti da ita wanda bayan isa likita ya tabbatar da cewa ta rigamu gidan gaskiya.
An kama wanda ya kashe tsohuwa a Bauchi
Biyo bayan mutuwar Safiya Yunusa ne yan sanda suka hada kai da yan banga wajen neman wanda ya kashe ta, rahoton Leadership.
Yan sanda sun kama Adamu Alhassan a bisa zargin kisan matar saboda dalilin samun takun kafarsa a gidanta da kuma makamin da aka kasheta da shi.
Rundunar yan sanda ta mika Adamu Alhassan ga sashen bincike domin kammala bincikensa da ɗaukan matakin da ya dace a kansa.
Yan sanda sun kama mahaifi a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya reshen a jihar Bauchi ta kama wani mahaifi da ya daure ɗansa da sarƙa da sunan koya masa tarbiyya.
Rahotanni sun yi nuni da cewa mutumin mai suna Mamuda Abubakar yana zaune ne a karamar hukumar Giade da ke jihar Bauchi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng