Wasu gungun marasa Imani sun yi ma tsohuwa yar shekara 70 kisan gilla da tabarya

Wasu gungun marasa Imani sun yi ma tsohuwa yar shekara 70 kisan gilla da tabarya

Ba mutuwa ake tsoro ba, wahalarta ake ji, anan ma wata tsohuwace ta yi rashin sa’a, inda ta gamu da ajalinta a hannun wasu gungun miyagun mutane a jahar Ondo, inda baya da kasheta da suka yi, suka yanke wasu sassan jikinta, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.com ta ruwaito an tsinci gawar wannan tsohuwa mai shekaru saba’in a duniya, Medinat Ala ne a dakinta dake gidanta a layin Okeegbe cikin unguwar Ikere Akoko a karamar hukumar Akoko ta Arewa ta basa dake jahar Ogun.

KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Daraktan daya shirya gadar zare, gagare, sangaya ya rasu

Sai dai rundunar Yansandan ta bayyana cewa ta kama guda daga cikin wadanda ake zargi da kisan, mai suna Moses Olaniyi, wanda Yansanda suka ce shi da wasu abokansa ne suka kashe Medinat a safiyar Laraba 21 ga watan Nuwamba, sa’annan suka yanke nonuwanta, mahaifanta da gabanta.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa: “Da tabarya suka halaka tsohuwar da sanyin safiyar Laraba, hakanan wani makwabciyarta da yayi kokarin ceton rayuwarta shima da kyar ya sha daga hannun miyagun mutanen, inda suka yanke mata sassan jiki don yin tsafi.

“Makwabciyar na zaune tare da tsohuwa Medina a cikin gidan, amma da ta ji ihun tsohuwar sai ta fito a guje don ta kai mata dauki, tana kokarin bude kofar dakin tsohuwar ne sai guda daga cikin miyagun ta buga mata tabarya a kai, nan take ta fadi sumamma, daga bisani aka garzaya da ita asibiti.” Inji shi.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Ondo, Femi Joseph ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace binciken farko farko ya nuna cewa miyagun sun dade suna shirya yadda zasu aikata kisan, inda suka bude kofar dakinta ba tare da hayaniya ba, sa’annan suka rufe kofar bayan sun kasheta.

Daga karshe kaakakin yace sun kaddamar da bincike akan mutumin da suka kama, kuma zasu dage har sai sun kai karshen lamarin, a yanzu haka gawar tsohuwa Medinat na ajiye a dakin ajiyan gawa na asibitin Ondo dake Ikare, Akoko.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: