Zargin Rashawa: Kotu Ta Yi Zama Kan Shari’ar El Rufai da Majalisar Jihar Kaduna
- Babbar kotun tarayya dake da zama a Kaduna ta dage sauraron karar da tsohon Gwamna El-Rufai ya shigar kan majalisar jihar
- Kotun ta ce dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Yulin 2024 bayan lauyoyin wadanda ake kara sun nemi haka
- Nasir El-Rufai ya nemi kotun ta bi masa kadinsa kan rahoton kwamitin majalisar dake nuna ya ci rashawa a yayin mulkinsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Babbar kotun tarayya dake da zama a Kaduna, ta dage sauraron ƙarar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shigar zuwa 17 ga Yulin 2024.
Nasir El-Rufai ne ya maka majalisar jihar Kaduna da Antoni Janar na jihar a gaban kotun inda yake kalubalantar rahoton kwamitin majalisar da ya nuna cewa ya saci kudin jihar.
Lauyoyin wadanda ake kara sun mika roko
Jaridar Daily Trust ta ruwaito lauyan majalisar Kaduna, Sani Kalu, SAN, ya sanar kotun cewa suna shirin shigar da sukar farko na nuna rashin hurumin kotun wurin sauraron ƙarar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sani Kalu sai ya bukaci karin lokaci domin basu damar shigar da dukkanin takardu na bukatunsu a kan karar da Nasir El-Rufai ya shigar.
Shi ma lauyan Antoni Janar na jihar, Sule Shuaibu, SAN, ya goyi bayan wannan bukatar da Sani Kalu ya gabatar.
Kotu ta yanke hukunci kan rokon lauyoyin
A bangarensa, lauyan mai kara, Sule Umoru, bai yi suka kan bukatar karin lokacin ba, kamar yadda rahoton Channels TV ya nuna.
Bayan sauraron bukatun da lauyoyin suka gabatar, Alkali Rilwan M. Aikawa, ya dage shari'ar zuwa ranar 17 ga Yulin 2024 domin baiwa wadanda ake kara damar shigar da bukatunsu.
Idan za a tuna, a ranar 26 ga watan Yunin 2024 muka ruwaito cewa Nasir El-Rufai ya shigar da kara gaban babban kotun tarayya dake a jihar Kaduna.
Yana kalubalantar rahoton binciken majalisar jihar Kaduna wanda ya bayyana cewa ya ci rashawa a mulkinsa na shekaru takwas.
Daga cikin ikirarinsu, ya bukaci kotun da ta wofantar da rahoton majalisar saboda take hakkinsa da aka yi. A cewarsa, majalisar ba ta bashi damar kare kansa kan zargin ba.
El-Rufai ya ki halartar taron APC
A wani labari na daban, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai, ya kauracewa taron jam'iyyar APC a jihar Kaduna.
An ruwaito cewa manyan jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar duk sun halarta, wadanda suka hada da kakakin majalisar wakiai, Abbas Tajudeen.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng