'Yan Ta'adda Sanye da Kayan Mata Sun Sace Mutane Masu Yawa a Katsina

'Yan Ta'adda Sanye da Kayan Mata Sun Sace Mutane Masu Yawa a Katsina

  • Ƴan ta'adda sun yi shigar mata tare da kai hari a ƙauyen Runka na ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Ƴan ta'addan sanye da hijabi sun yi awon gaba da mutane 26 da suka haɗa da mata da ƙananan yara a yayin harin da suka kai
  • Shugaban ƙaramar hukumar Safana, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun shammaci mutane

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Wasu ƴan ta’adda da suka yi shigar mata sanye da hijabi sun yi garkuwa da mutane 26 a jihar Katsina.

Ƴan ta'addan sun kai harin ne a ƙarshen mako a ƙauyen Runka cikin ƙaramar hukumar Safana inda suka yi awon gaba da mutanen galibinsu mata da ƙananan yara.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yiwa jami'an tsaro kwanton bauna, sun hallaka mutum 4

'Yan ta'adda sun sace mutane a Katsina
'Yan ta'adda sun sace mutum 26 a Katsina Hoto: Legit.ng
Asali: Original

'Yan bindiga sun dauke mutane a Katsina

Wani mazaunin yankin ya ce ƴan ta'addan sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare, inda suka riƙa yin harbe-harbe, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A gidana kaɗai sun sace mata 10 da maza biyu. Gaba ɗaya, sun sace jimillar mutane 26 "

- Wata majiya

Ya alaƙanta harin da munanan ayyukan masu ba ƴan ta'adda bayanai waɗanda ake haɗa baki da su wajen yin zagon ƙasa ga ƙoƙarin gwamnati na yaƙi da ƴan ta’adda.

Me hukumomi suka ce kan harin?

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin shugaban ƙaramar hukumar Safana, Abdullahi Sani Safana, ya shaida wa manema labarai cewa an yi garkuwa da mutanen yankin 22, amma wasu sun kuɓuta.

Ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun shammace su ne bayan sun yi baɗɗa kama sanye da hijabai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi dare sun sace 'yan jarida 2 tare da iyalansu a Arewa

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq, sai dai bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Karanta wasu ƙarin labaran kan ƴan ta'adda

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta da ke yaƙi da ta'addanci a jihar Kaduna, sun yi nasarar daƙile wani harin ƴan ta'adda.

Rundunar ta ce dakarun sun kuma yi nasarar hallaka ƴan ta'adda mutum biyu bayan sun yi musu kwanton ɓauna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng