LGBTQ: Gwamnatin Kano Ta Ba Hisbah Umarni Kan Masu Tallata Auren Jinsi

LGBTQ: Gwamnatin Kano Ta Ba Hisbah Umarni Kan Masu Tallata Auren Jinsi

  • Gwamnatin jihar Kano ta ba hukumar Hisbah umarnin cafke duk wata kungiya da aka samu tana tallatawa ko rajin kare masu auren jinsi
  • A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Abba Yusuf ya fitar, gwamnatin ta ce tallata auren jinsi ya sabawa dokokin jihar
  • Idan ba a manta ba, dama gwamnatin jihar ta ce ta fara gudanar da bincike kan wata kungiya da aka gano tana tallata auren jinsi a Kano

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta sake daukar mataki kan wasu kungiyoyi da ake zargin suna rajin kare 'yancin masu auren jinsi a jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba hukumar Hisbah umarnin ganin bayan duk wata kungiya da take tallata auren jinsi a fadin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Auren jinsi: Yadda kururuwar mutanen Kano ya dakile yunkurin kungiyar LGBTQ

Gwamnatin Kano ta ba da umarnin cafke kungiyoyin da ke tallata auren jinsi
Gwamna Abba Yusuf ya ba Hisbah umarnin cafke masu tallata auren jinsi a Kano. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Facebook

Kano: Za a kama masu tallar auren jinsi

Mai tallafawa gwamnan ta fuskar kafofin sada zumunta, Abdullahi I. Ibrahim ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi Ibrahim ya ce:

"Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya umurci hukumar Hisbah da ta cafke kungiyoyin da ake zargi da tallatawa da kuma fafutukar kare hakkin masu auren jinsi a Kano."

Sanarwar ta ce tallatawa ko kuma kare 'yancin masu auren jinsi ta hanyar bayyanawa a fili ya saba da dokar jihar Kano.

Duba sanarwar a kasa:

Bullar kungiyar WISE a jihar Kano

Tun da fari, mun ruwaito cewa an samu bullar wata kungiya da ake kira WISE wadda ake zargin tana tallatawa da kuma rajin kare masu auren jinsi a jihar Kano.

Hassan Sani Tukur, mai tallafawa Gwamna Abba Yusuf a fuskar kafofin sadarwa ya ce gwamnatin jihar na sane da bullar wannan kungiyar kuma ta sa ayi bincike.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya dauki mataki kan bullar wata kungiya mai tallata alakar jinsi

A cewar Hassan Tukur:

"Gwamnatin Kano ta samu masaniya game da wata kungiya da ke tallatawa da kuma rajin kare masu auren jinsi. Kuma tun jiya aka fara bincike.
Muna so mu tabbatar wa kowa da kowa cewa Kano a karkashin jagorancinmu da kowace gwamnati mai zuwa ba za ta taba amincewa da wannan danyen aikin ba."

Gwamnati ta kare kanta kan Samoa

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta sake fitowa ta kare kanta kan yarjejeniyar Samoa da ta sanyawa hannu, inda ta ce babu batun auren jinsi a ciki.

Ministan yada labarai da wayar da kai, Mohammed Idris ya ce kwata-kwata babu batun auren jinsi ko a ce Najeriya ta karbi bashin $150bn a cikin yarjejeniyar Samoa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.