"Babu Ruwanmu Da Bambancin Addini," Rundunar Sojoji ta Karyata Zargin Wariya

"Babu Ruwanmu Da Bambancin Addini," Rundunar Sojoji ta Karyata Zargin Wariya

  • Rundunar sojojin Najeriya ta musanta cewa ta na nuna wariyar addini ga jami'anta, inda ta ce babu gaskiya cikin labarin da ake yadawa
  • Daraktan hulda da jama'a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka a matsayin martani ga masu zarginsu da wariya
  • Ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a lamarin domin sun ba wa dukkanin jami'ansu damar gudanar da addini ba tare da katsalandan ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Rundunar sojojin Najeriya ta jaddada matsayarta na rashin yi wa jami'anta katsalandan kan addininsu.

Rundunar ta bayyana cewa a matsayinta na hukumar da ke ba wa kowa damar gudanar da addininsa, ba ta nuna wariyar addini.

Kara karanta wannan

An kama jagora a PDP, Atiku Abubakar ya zargi 'yan sanda da cin zarafin 'yan kasa

Rundunar sojoji
Rundunar sojojin kasar nan ta musanta wariyar addini tsakanin jami'anta Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa daraktan hulda da jama'a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka ta cikin sanarwar da ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar soja ta musanta fifita musulmi

Rundunar sojojin kasar nan ta musanta cewa musulmi kawai ta ke dauka a makarantar koyon aikin sojojin Najeriya, The Guardian ta wallafa.

Daraktan hulda da jama'a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne ya yi martanin haka kan rahoton cewa musulmai su ka fi dauka a makarantunsu.

Ya ce a matsayinsu na runduna mai kare martabar kowa da 'yancin addini, ba a nuna kyama ko hana wani jami'inta gudanar da addininsa.

Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya kara da cewa akwai cibiyoyin rundunar daban-daban, kuma ba sa hana kowane jami'i yin addininsa.

Sojoji sun hallaka 'yan ISWAP

Kara karanta wannan

Mahaifiyar Rarara ta rasa ranta a hannun ƴan bindiga? Gaskiya ta bayyana

A wani labarin kun ji cewa jami'an sojojin kasar nan sun hallaka 'yan ta'addan ISWAP 11 a wani artabu da suka yi a jihar Borno.

Jami'an sun samu nasarar ne a wani samamen hadin gwiwa da su ka kai maboyar 'yan ta'addan da ke dajin Sambisa, inda su ka ragargajesu.

An kuma samu nasarar kwace mugayen makamai da su ka hada da bindigogi da albusari daga maboyar 'yan ta'addan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.