An Kama Mahaifin da Ya Daure Dansa Bayan Sun Rabu da Mahaifiyar Yaron
- Rundunar yan sandan Najeriya reshen a jihar Bauchi ta kama wani mahaifi da ya daure ɗansa da sarƙa da sunan koya masa tarbiyya
- Rahotanni sun yi nuni da cewa mutumin mai suna Mamuda Abubakar yana zaune ne a karamar hukumar Giade da ke jihar Bauchi
- Mamuda Abubakar ya bayyana cewa sun rabu da mahaifiyar yaron ne shekara biyar da suka wuce kuma ya nace da zuwa wajen yan uwanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta yi nasarar cafke wani mutum bisa zargin muzgunawa dansa.
Mahaifin mai suna Mamuda Abubakar ya bayyanawa yan sanda dalilin daure dan nasa yayin da ake bincikensa.
Legit ta tatttaro labarin ne a cikin wani sako da rundunar yan sandan jihar Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama mahaifin da ya daure ɗansa
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa Mamuda Abubakar ya daure dan cikinsa cikin sarƙa wanda laifi ne a dokar kasa.
A dalilin haka ne rundunar yan sanda ta yi nasarar cafke Mamuda Abubakar a a jiya Lahadi, 7 ga watan Yuli.
Yan sanda sun kama mahaifin ne a yankin Abbo a unguwar Chinkani a karamar hukumar Giade da ke jihar Bauchi.
Meyasa mahaifi ya daure ɗansa?
A yayin da yan sanda ke gudanar da bincike, mahaifin ya bayyana cewa sun rabu da mahaifiyar yaron ne tun shekaru biyar da suka wuce.
Shi kuma yaron kullum yana yunkurin zuwa gidan kakarsa bayan mahaifiyarsa ta riga ta yi sabon aure.
Mahaifin ya kuma tabbatar da cewa yana tsoron tarbiyyar yaron ta lalace idan yana zuwa gidan, wannan ya sa ya daure shi a gida.
An kama barawo a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta cafke babban ɓarawo da ake zargin ya fitini al'umma da sace-sace.
Ɓarawon mai suna Glory Samuel ya sace makudan kudi da kayayyaki na miliyoyin kudi daga mutane da dama a jihar Bauchi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng