NELFund ta Lissafa Makarantu Mallakar Jihohi Da Za Su Samu Lamunin Karatu

NELFund ta Lissafa Makarantu Mallakar Jihohi Da Za Su Samu Lamunin Karatu

  • Dalibai a wasu daga cikin makarantun jihohi za su iya fara neman tallafi karatu daga gwamnatin tarayya
  • Hukumar NELFund ce ta bayyana haka ta sakon da ta wallafa a shafinta na X, inda ta lissafa makarantun da za su samu
  • Hukumar ta kara da cewa daga ranar 7 Yuli, 2024 aka bude shafinta da dalibai za su shiga domin cike bayanan neman lamunin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Hukumar kula da asusun bayar da lamunin karatu ta kasa (NELFUND) ta bayyana cewa dalibai daga makarantu mallakar jihohin kasar nan 36 za su samu lamunin karatu gwamnati. Haka kuma hukumar ta bayyana cewa daliban za su fara iya neman lamunin karatun daga ranar 7 Yuli, 2024.

Kara karanta wannan

An jibge motocin jami'an tsaro domin kare ofishin EFCC daga masu zanga zanga

Students
Dalibai daga manyan makarantu mallakin jihohi za su iya fara neman lamunin karatu Hoto: Good Boy Picture Company
Asali: Getty Images

A sakon da ta wallafa a shafinta na X, hukumar NELFUND ta lissafa jami'o'i da manyan makarantun jihohi da ke cikin tsarin bayar da lamunin karatun.

Jami'o'i ne kaɗai za su samu lamunin?

Hukumar kula da asusun bayar da lamunin karatu NELFUND ta bayyana cewa wasu manyan makarantu mallakin jihohi sun bayar da bayanan dalibansu. Ba jami'o'i ne kawai a tsarin ba, domin daga jerin manyan makarantun da NELFUND ta wallafa akwai makarantun kimiyya da fasaha, The Cable ta wallafa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makarantu da za su samu lamunin karatu

Hukumar NELFUND ta wallafa sunayen manyan makarantu mallakin jihohi da za su iya neman tallafin karatun gwamnatin tarayya.

Manyan makarantun sun hada da;

1. Adamawa State University, Mubi 2. Ramat Polytechnic, Maiduguri 3. Borno State University 4. Mohammed Lawan College of Agriculture, Borno 5. Edo State University, Uzairue 6. Ekiti State University, Ado-Ekiti 7. Gombe State University 8. Kingsley Ozumba Mbadiwe University, Imo 9. Imo State University of Agriculture and Environmental Sciences Umuagwo 10. Nuhu Bamalli Polytechnic, Zaria 11. Yusuf Maitama Sule University, Kano 12. Umaru Musa Yar’adua University, Katsina 13. Katsina State Institute of Technology and Management 14. Kebbi State University of Science and Technology, Aliero 15. Confluence University of Science and Technology, Kogi state 16. Lagos state university of education 17. Lagos State University 18. Nasarawa State University, Keffi 19. Tai Solarin University of Education, Ogun state 20. University of Medical Sciences, Ondo 21. Osun State University 22. University of Ilesa, Osun 23. GTC, ARA Osun State 24. GTC, GBONGAN Osun 25. GTC, IJEBU-JESA Osun 26. GTC, ILE-IFE Osun 27. GTC, INISA Osun 28. GTC, IWO Osun 29. GTC,OSU Osun 30. GTC, OTAN AYEGBAJU Osun 31. Osun State College of Education, Ila-Orangun 32. Government Technical College Ile-Ife 33. Osun State College of Technology 34. Taraba State University, Jalingo 35. Umar Suleiman College of Education, Gashua, Yobe State 36. Zamfara State University, Talata Mafara

Kara karanta wannan

Yan sandan Kano sun cafke 'yan bindiga da 'yan daba sama da 100 cikin kwanaki 10

Lamunin karatu: NELFUND ta dakatar da jihohi

A baya, kun ji cewa hukumar NELFUND ta dakatar da manyan makarantu mallakin jihohi daga neman lamunin karatu.

Hukumar ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda kadan ne daga manyan makarantun jihohi su ka bayar da bayanan dalibansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.