Yayin Ake Yawan Korafi, Gwamnati Za Ta Samar da Dokar Haramta Barace Barace

Yayin Ake Yawan Korafi, Gwamnati Za Ta Samar da Dokar Haramta Barace Barace

  • Gwamnatin jihar Lagos tana kokarin samar da wata doka domin haramta barace-barace a fadin jihar baki daya
  • Kakakin Majalisar jihar, Mudashiru Obasa shi ya tabbatar da haka inda ya ce dokar za ta ba gwamnatin jihar ikon dakile matsalar
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake yawan korafe-korafe kan masu bara a fadin jihar da ma sauran jihohin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Kakakin Majalisar jihar Lagos, Mudashiru Obasa ya magantu kan yiwuwar samar da dokar hana barace-barace.

Obasa ya ce dokar idan an tabbatar da ita za ta haramta yawan barace-barace da ake yi a fadin jihar.

Gwamnati za ta samar da dokar haramta bara
Gwamnatin jihar Lagos tana shirin samar da dokar haramta barace-barace. Hoto: Mudashiru Obasa.
Asali: Facebook

Lagos: Za a yi dokar haramta bara

Kara karanta wannan

Gwamna ya lashe amansa kan taimakon masallaci, ya shawarci Musulmai kan ba da Zakka

Kakakin Majalisar ya bayyana haka ne yayin kaddamar da kungiyar Zakka da Wakafi ta Ibile Muslims Community, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya kamata a samar da dokar domin dakile matsalar baki daya a jihar wanda ya yi kamari.

Har ila yau, ya ce dokar za ta ba gwamnatin jihar karfin iko da kuma irin wadannan Gidauniyar dakile bara, Daily Post ta tattaro.

"Muna neman hanyar kawo wani tsari da zai dakile barace-barace a kan hanyoyin Lagos.'
"Bayan samar da dokar, duk wanda aka kama da aikata laifin musamman kananan yara za su fuskanci hukunci."

- Mudashiru Obasa

Lagos: Wuraren da dokar za ta taba

Obasa ya ce samar da dokar ya zama dole ganin yadda kullum mabaratan ke kara yawa a fadin jihar baki daya.

Ya ce dokar har ila yau, za ta tabbatar tallafi ya isa wurin mabukata ba tare da sai sun je kan hanyoyi suna bara ba.

Kara karanta wannan

Samoa: Tinubu zai dauki mataki kan Daily Trust game da rahoton yarjejeniyar da aka yi

Gwamna Sanwo-Olu ya shawarci Musulmai kan Zakka

A wani labarin mai kama da wannan, Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya shawarci Musulmai kan ba da Zakka.

Sanwo-Olu ya hori alummar Musulmai da su rinƙa ba da Zakka da kuma taimakon marasa karfi a yankunansu.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna ya sha suka kan kalamansa da ya ce kada 'yan fasnho su ba da taimakon masallaci da coci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.