Abu Namu: CJN Zai Rantsar da Surukarsa da Matar Ministan Tinubu Manyan Alkalai

Abu Namu: CJN Zai Rantsar da Surukarsa da Matar Ministan Tinubu Manyan Alkalai

  • Shugaban alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola ya shirya rantsar da sababbin alkalan Babbar Kotun Tarayya a Abuja
  • Mai Shari'a Ariwoola zai rantsar da sababbin alkalan ne guda 12 a ranar da Laraba 10 ga watan Yulin 2024 a birnin
  • Daga cikin wadanda za a rantsar din akwai surukar shugaban alkalan da kuma matar Ministan Abuja, Nyesom Wike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban alkalan Najeriya, Mai Shari'a, Olukayode Ariwoola zai rantsar da sababbin alkalan Babbar Kotun Tarayya 12.

Ariwoola zai rantsar da su ne a ranar Laraba mai zuwa 10 ga watan Yulin 2024 da muke ciki.

Za a rantsar da sababbin alkalan Babbar Kotu 12 a Najeriya
Shugaban alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola zai rantsar da sababbin alkalan Babbar Kotu. Hoto: Justice Olukayode Ariwoola, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Ariwoola zai rantsar da sababbin alkalai 12

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban kungiyar NLC, an samu bayanai

Daraktan yada labaran Kotun Koli, Dakta Festus Akande shi ya bayyana haka ga manema labarai a yau Lahadi 7 ga watan Yulin 2024, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akande ya ce za a gudanar da taron rantsarwar ne a dakin shari'a da ke Kotun Koli da misalin karfe 10 na safe.

Punch ta tattaro cwa daga cikin alkalan guda 12 da za a rantsar akwai surukar Ariwoola mai suna Oluwakemi Victoria Ariwoola.

Sai kuma matar Ministan Abuja, Nyesom Wike mai suna Lesley Nkesi Belema Wike.

Jerin alkakan za a rantsar

1. Ariwoola Oluwakemi Victoria (Oyo)

2. Ademuyiwa Olakunle Oyeyipo (Kwara)

3. Bamodu Odunayo Olutomi (Lagos)

4. Iheabunike Anumaenwe Godwin (Imo)

5. Odo Celestine Obinna (Enugu)

6. Hauwa Lawal Gummi (Zamfara)

7. Sarah Benjamin Inesu Avoh (Bayelsa)

8. Maryam Iye Yusuf (Kogi)

Kara karanta wannan

Samoa: Tinubu zai dauki mataki kan Daily Trust game da rahoton yarjejeniyar da aka yi

9. Buetnaan Mandy Bassi (Plateau)

10. Lesley Nkesi Belema Wike (Rivers)

11. Ibrahim Tanko Munirat (Bauchi)

12. Abdulrahman Usman (Taraba).

Wike ya yi barazana ga Sanata Kingibe

A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya sha alwashin kayar da Sanata Ireti Kingibe a zaben 2027 da ke tafe.

Minista Wike ya ce zai nuna mata shi ne ke jagorantar birnin Abuja ba kamar lokacin da ta yi nasara a zaben 2023 ba.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takun saka tsakanin Nyesom Wike da kuma Sanata Kingibe da ta yi nasara a jam'iyyar LP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.