Gwamna Radda Ya Nemi Wata Alfarma Wajen Mutanen Katsina Kan Matsalar Tsaro
- Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya aika da saƙon taya al'ummar musulmi murnar shigar sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH
- Gwamna Radda ya buƙaci al'ummar jihar da su yi amfani da lokacin wajen yin addu'o'i domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar
- Ya buƙaci al'ummar jihar da su koma ga Allah domin samun mafita kan matsalar rashin tsaron wacce ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa a jihar da wasu jihohi na yankin Arewa maso Yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya buƙaci al'ummar jihar da su yi addu'o'i domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.
Gwamna Dikko Radda ya buƙaci al'ummar musulmin su roƙi Allah maɗaukakin Sarki ya kawo ƙarshen matsalar wacce ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa.
Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a cikin saƙon murnar shiga sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH, wanda sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ibrahim Mohammed ya fitar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane kira Gwamna Radda ya yi?
"Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umaru Radda yana taya ɗaukacin ƴan uwa Musulmi murnar zagayowar wannan sabuwar shekarar Hijira ta 1446."
"Gwamnan ya yi kira ga ɗaukacin al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokacin wajen zurfafa tunani da mayar da hankali ga koyarwar addinin musulunci."
"Gwamnan ya yi kira ga al'umma da su yi amfani da wannan lokaci na musamman wajen gudanar da addu’o’i ga jihar Katsina."
"Mu roƙi Allah ya ba mu hikima da ƙarfin gwiwar da za mu yi kawo ƙarshen matsalar rashin da ta addabi yankinmu."
- Ibrahim Mohammed
Gwamna Radda ya kawo mafita kan albashin ma'aikata
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa ya kamata a bar kowace gwamnatin jiha ta tsara mafi ƙarancin albashinta.
Gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa a Najeriya ne kaɗai ake amfani da tsarin mafi ƙarancin albashi na bai ɗaya ba tare da bambantawa ba.
Asali: Legit.ng