Tinubu Zai Sauka Daga Kujerar Shugaban Kungiyar ECOWAS Yayin da Wa’adinsa Ya Kare

Tinubu Zai Sauka Daga Kujerar Shugaban Kungiyar ECOWAS Yayin da Wa’adinsa Ya Kare

  • A yau Lahadi, 7 ga watan Yulin 2024 ne ake sa ran shugabannin kungiyar yammacin Afrika (ECOWAS) za su zabi sabon shugaba
  • Wannan na zuwa ne bayan wa'adin shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin shugaban kungiyar ECOWAS ya zo karshe
  • Sai dai akwai rade-radin cewa shugabannin kungiyar na iya ba Shugaba Tinubu damar ci gaba da jan ragamar kungiyar karo na biyu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa a yau Lahadi ne wa’adin shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin shugaban kungiyar ECOWAS ya zo karshe.

Mun ruwaito cewa mambonin shugabannin ECOWAS sun amince da Tinubu a matsayin shugaba a babban taronta karo na 63 a kasar Guinea-Bissau.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban kungiyar NLC, an samu bayanai

A yau Lahadi ne ake sa ran wa'adin Shugaba Bola Tinubu zai kare daga shugabancin ECOWAS
A yau Lahadi ne kungiyar ECOWAS za ta zabi shugaba bayan karewar wa'adin Shugaba Tinubu. Hoto: @ecowas_cedeao
Asali: Twitter

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa ana kan gudanar da taron ECOWA na 65 a fadar shugaban kasa dake Abuja inda ake sa ran zai Tinubu zai mika mulki ko kuma ya nemi tazarce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai yiwuwar Tinubu ya zarce

A taron wanda aka shirya fara shi da karfe 11:00 na safe ne ake sa ran shugabannin ECOWAS za su zabi sabon shugaban da zai jagoranci harkokin kungiyar a shekara mai zuwa.

Sai dai jaridar The Punch ta ce akwai alamu da ke nuna cewa shugabannin na iya tsawaita wa’adin Tinubu domin ba shi lokaci dawo da kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso cikin kungiyar.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa da ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da izinin yin magana a kan lamarin ta shaida wa jaridar cewa:

“Wasu na cewa Shugaba Bola Tinubu ya mika mulkin kungiyar kawai, yayin da wasu kuma na cewa ya ci gaba da shugabancinta. Amma dai ranar Lahadi za a tantance."

Kara karanta wannan

Sanatocin kudu maso gabas sun gana da Ministan shari'a domin a saki Nnamdi Kanu

Mulkin Tinubu a kungiyar ECOWAS

Idan ba a manta ba, tun bayan hawansa shugaban ECOWAS Shugaba Tinubu yake fama da matsalolin juyin mulkin da sojoji suka yi a kasashe 3 na kungiyar.

Da farko dai shugaban ya dauki matsaya mai karfi kan juyin mulkin gwamnati da aka yi a jamhuriyar Nijar, Burkina Faso, Mali da kuma Guinea, inda ya saka musu takunkumi.

Sai dai daga baya an dage takunkumin a yayin da kungiyar ECOWAS ta zabi samar da hanyar lumana domin warware matsalolin kasashen.

Shugaba Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar zaben Senegal na 2024 ta hanyar gudanar da tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki.

Yawan kasashen ECOWAS ya kai 15

A wani labarin, mun ruwaito cewa binciken da Legit Hausa ta yi a shafin yanar gizon ECOWAS ya nuna cewa har yanzu kasashe 15 ne a jerin kasashen da ke a cikin kungiyar.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kungiyar yammacin Afrika (ECOWAS) ta dage takunkumin karya tattalin arzikin da ta kakabawa Nijar, Mali da Burkina Faso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.