Samoa: Sheikh Gumi Ya Yi Martani Kan Yarjejeniyar, Ya Shawarci Gwamnati

Samoa: Sheikh Gumi Ya Yi Martani Kan Yarjejeniyar, Ya Shawarci Gwamnati

  • Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi ya yi magana kan cece-kucen da ake yi game da yarjejeniyar Samoa
  • Sheikh Gumi ya ce bayan samun labarin yarjejeniyar ya kira Minista Atiku Bagudu inda ya nemi bahasi kan lamarin
  • Malamin ya ce ya ga yarjejeniyar a bayyane babu auren jinsi amma maganar gaskiya a kunshe akwai maganar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Sheikh Ahmed Gumi ya yi martani kan yarjejeniyar Samoa da gwamnati ta sanyawa hannu.

Sheikh Gumi ya yi gargadi kan lamarin inda ya ce manakisar Turawa ta wuce yadda mutane ke tunani.

Sheikh Gumi ya magantu kan yarjejeniyar Samoa da ake ta cece-kuce a kai
Sheikh Gumi ya bayyyana matsayarsa kan yarjejeniyar Samoa. Hoto: Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Samoa: Sheikh Gumi ya yi martani

Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da @el_uthmaan ya wallafa a shafin X a yau Lahadi 7 ga watan Yulin 2024.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu: Sheikh Dutsen Tanshi ya dauki zafi kan rigimar Kano, ya fadi matsayarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya ce ya duba yarjejeniyar tabbas babu auren jinsi amma akwai ta a kunshe watakila son kudi ya rufewa gwamnatin ido.

Ya bayyana cewa idan Turawa ne za su iya yaudararsu babu auren jinsi da zarar an zo karbar kudi sai magana ta sauya.

Sheikh Gumi ya yi gargadi kan Samoa

"Daga samun labarin rahoton Daily Trust na cewa an sanya hannu kan yarjejeniyar na kira Minista Atiku Bagudu inda ya tabbatar babu auren jinsi a ciki."
"Ya ce kafin rattaba hannun sun samu ma'aikatu guda uku suka duba suka tabbatar babu abin da ya shafi auren jinsi a ciki."
"Daga baya an turomin yarjejeniyar na gani, maganar gaskiya a bayyane babu amma a kunshe akwai."
"Watakila idon gwamanti ya rufe saboda son kudi ba su kula da hakan ba saboda suna ganin za su yiwa Turawa wayo."

Kara karanta wannan

Samoa: Gwamnati ta magantu kan ikirarin 'yan Arewa za su guji Tinubu a 2027

- Sheikh Ahmed Gumi

Jingir ya fusata kan yarjejeniyar Samoa

Kin ji cewa Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi martani mai zafi kan yarjejeniyar Samoa da Gwamnatin Tarayya ta sanyawa hannu a makon jiya.

Sheikh Jingir ya ce al'ummar Musulmai da na Kiristoci duka ba su amince da wannan tsari ba kuma ba za su yarda ba inda ya ce dole a janye dokar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.