Dangote Ya Biya Naira Miliyan 100 Domin Maido da Wutar Lantarki a Jami’ar Kano

Dangote Ya Biya Naira Miliyan 100 Domin Maido da Wutar Lantarki a Jami’ar Kano

  • Hukumar gudanarwar jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke jihar Kano ta sanar da maido da wutar lantarki a jami'ar
  • Kamfanin KEDCO ya maido da wuta a jami'ar ne biyo bayan shiga tsakani da gwamnatin jihar Kano da gidauniyar Dangote suka yi
  • An ruwaito cewa gidauniyar Aliko Dangote ta biya N100m ga KEDCO domin maido da wutar, kuma wutar ta dawo ranar Juma'a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Kamfanin Kano Electric (KEDCO) ya sake dawo da wutar lantarki da jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, bayan an biya shi Naira miliyan 100.

Shugaban jami’ar ADUSTECH, Farfesa Musa Yakasai, ya tabbatar da maido da wutar lantarkin a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

An sha dakyar: Wutar lantarki ta gyaru, an ga dawowar wuta a wasu jihohin Najeriya

Aliko Dangote ya biya N100m domin maido da wuta a jami'ar Kano
Aliko Dangote ya biya kamfanin KEDCO Naira miliyan 100 domin maido da wuta jami'ar Kano. Hoto: Aliko Dangote University
Asali: Twitter

ADUSTECH: Dangote ya biya KEDCO N100m

Farfesa Yakasai ya ce an maido da wutar lantarki a jami'ar da misalin karfe hudu na yamma bayan an biya kusan Naira miliyan 100, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin KEDCO ya dauki matakin datse wutar ne duk da biyan Naira miliyan 20 daga cikin Naira miliyan 60 da jami’ar Aliko Dangote ke biya duk wata.

Farfesa Yakasai ya ce an dawo da wutar ne bayan ne da tsoma bakin gwamnatin jihar Kano da gidauniyar Dangote, waddata ta fara biyan Naira miliyan 100 ga KEDCO.

Jami'ar Aliko Dangote ta magantu

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito gwamnatin Kano ta kuduri aniyar biyan basussukan wutar, yayin da gidauniyar Dangote ke neman dora jami'ar a kan tsarin wutar lantarki daga rana.

Hukumar gudanarwar jami’ar ta yi godiya ga duk wadanda suka saka hannu wajen dawo da wutar tare da yin kira ga mazauna jami'ar da su yi amfani da wutar yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Karin kudin lantarki: Kungiyar NLC ta aika sabuwar bukata ga gwamnatin Tinubu

KEDCO ta datse wutar jami'ar Kano

Tun da fari, mun ruwaito cewa kamfanin Kano Electric (KEDCO) ya yanke wutar jami'ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote saboda tarin bashin da ta gaza biya.

Da yake sanar da halin da ake ciki ga manema labarai, shugaban sashen kula da harkokin dalibai na jami’ar, Farfesa Abdulkadir Dambazau, ya ce sun dogara ne kan wutar KEDCO.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.