Gwamna Ya Fusata Kan Jami'an Gwamnati da Suka Karkatar da Kudaden Ma'aikata, Ya Ba su Umarni

Gwamna Ya Fusata Kan Jami'an Gwamnati da Suka Karkatar da Kudaden Ma'aikata, Ya Ba su Umarni

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta ware kuɗaɗe domin rabawa ma'aikata a matsayin goron Sallah a lokacin bukukuwan babbar Sallah
  • Gwamna Ahmed Aliyu ya gargaɗi jami'an gwamnati da suka karkatar da kuɗaɗen da su gaggauta dawo da su
  • Ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu gurɓatattun jami'ai musamman a matakin ƙananan hukumomi suka karkatar da kuɗaɗen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya umarci jami’an gwamnati da su mayar da kuɗaɗen da suka karkatar na goron Sallah da aka ba ma'aikata.

Gwamnan ya umarce su da su mayar da N30,000 da aka ware domin ba kowane ma'aikaci ko su fuskanci hukunci mai tsauri.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Gwamnatin Tinubu ta tuna da mutanen da sojoji suka jefa wa bam a Kaduna

Gwamnan Sokoto ya gargadi jami'an gwamnati
Gwamna Ahmed Aliyu ya umarci jami'an su dawo da kudaden ma'aikata da suka karkatar Hoto: @Ahmedaliyuskt
Asali: Facebook

Gwamnan ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Juma’a a lokacin da yake jawabi ga ɗumbin jama’a da magoya bayansa a gidan gwamnati, da ke Sokoto, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane gargaɗi gwamnan ya yi?

Ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu jami’an kuɗi musamman a matakin ƙananan hukumomi suka hana ma’aikata N30,000 da gwamnatin jihar ta amince da su a matsayin goron Sallah, rahoton Daily Post ya tabbatar.

"Ina mamakin yadda wani zai hana ma’aikatanmu alawus ɗin da muka ba su domin su yi walwala a lokacin bukukuwan Sallah.
"Waɗanda suka karkatar da waɗannan kuɗaɗe dole ne su dawo da su cikin gaggawa idan ba haka ba za mu ɗauki tsauraran matakan ladabtarwa a kansu."
"Za mu tabbatar da cewa masu laifin sun girbi abin da suka shuka domin ya zama darasi ga saura."

Kara karanta wannan

Muhammadu Sanusi II ya faɗi yadda za a magance matsalolin da suka addabi Najeriya

- Ahmed Aliyu Sokoto

Gwamnan ya kuma buƙaci dukkanin shugabannin hukumomin da aka yi wannan ɓarnar da su gaggauta tattara duk ma’aikatan da abin ya shafa tare da tabbatar da an mayar musu da kuɗaɗensu.

Gwamnan Sokoto na iya rasa kujerarsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto na daga cikin gwamnonin da ke wa'adinsu na farko kan kujerar mulki.

Wasu na ganin gwamnan ka iya rashin nasara a zaɓen 2027 saboda wasu matakai da ya ke dauka a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng