Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana Kan Yiwa 'Yan NYSC Karin Alawus

Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana Kan Yiwa 'Yan NYSC Karin Alawus

  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ce matasan da ke yiwa ƙasa hidima za su samu ƙarin alawus na wata-wata daidai da mafi ƙarancin albashi da aka amince da shi
  • Shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Y.D Ahmed ya bayyana hakan a madadin gwamnatin Tinubu a ziyarar da ya kai sansanin horar da masu yiwa ƙasa hidima a jihar Ogun
  • Y.D Ahmed ya gargaɗi masu yiwa ƙasa hidimar da su daina tafiye-tafiye ba tare da izini ba da yaɗa abubuwan da ke faruwa sansanin horarwar a shafukan sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ijebu-Ode, jihar Ogun - Gwamnatin tarayya ta shugaban ƙasa Bola Tinubu ta yi magana kan yiwa matasa masu yiwa ƙasa hidima (NYSC) ƙarin kuɗaɗen alawus.

Kara karanta wannan

Ana batun yarjejeniyar samoa, Tinubu ya fadi abin kunyar da Najeriya ta yi

Gwamnatin ta ce matasan za su ci gajiyar sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata idan majalisar tarayya ta amince da shi.

'Yan NYSC za su samu karin alawus
Gwamnati za ta yiwa 'yan NYSC karin alawus @OfficialABAT, @Officialnyscng
Asali: Twitter

Za a yiwa ƴan NYSC ƙarin alawus

Gwamnatin ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Y.D Ahmed, a sansanin horar da masu yiwa ƙasa hidima na jihar Ogun a ranar Asabar, 6 ga watan Yulin 2024, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Daily Independence ta ruwaito, shugaban na NYSC bayyana cewa masu yiwa ƙasa hidimar za su amfana idan sabon mafi ƙarancin albashin ya zama doka.

"Dangane da alawus ɗin ku, ka da ku damu da zarar an kammala tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashin zai ƙaru. Babu yadda za a yi gwamnati ta manta da ku saboda ku ɗin na musamman ne."

Kara karanta wannan

EFCC ta bankado makarkashiyar da ake kulla mata, hukumar ta aika da gargadi

- Birgediya Y.D Ahmed

Shugaban NYSC ya gargaɗi masu yiwa ƙasa hidima

Ya kuma gargaɗi matasa masu yiwa ƙasa hidima da su daina yaɗa hotunan abubuwan da ke faruwa a sansanin a shafukan sada zumunta, inda ya ce tuni kori mambobi uku saboda karya wannan doka.

Birgediya-Janar Ahmed, ya gargaɗi matasan kan yin tafiye-tafiye ba tare da izini ba a lokacin da suke hidimtawa ƙasa.

Ya kuma jaddada cewa abin da hukumar ta mayar da hankali a kai shi ne tabbatar da cewa matasan sun koma gidajensu lafiya bayan kammala hidimtawa ƙasa.

Gwamna ya ɗauki ƴan NYSC aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ɗauki matasa masu yiwa ƙasa hidima aiki, waɗanda suka karanci likitanci da sauran fannonin kiwon lafiya.

Umaru Bago ya sanar da cewa gwamnatinsa ta ɗauke su aiki ne domin kawo ƙarshen mutuwar likitoci da sauran malaman lafiya a asibitocin jihar Neja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng