'Yan Sanda Sun Ragargaji Masu Garkuwa da Mutane a Jihar Delta

'Yan Sanda Sun Ragargaji Masu Garkuwa da Mutane a Jihar Delta

  • Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Delta sun samu nasara kan wasu gungun masu laifi da ake zargi da yin garkuwa da mutane
  • An cafke waɗanda ake zargin ne bayan sun sace wani mutum tare da hallaka shi a ƙaramar hukumar Ughell ta Kudu a jihar
  • Ƴan sanda sun hallaka ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin yayin da suka yi nasarar cafke sauran mutum uku

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Delta sun dira kan wasu gungun mutane huɗu da ake zargin masu garkuwa da mutane.

Jami'an ƴan sandan sun cafke mutanen da ake zargin ne a yankin Ughelli da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka 'yan gudun hijira bayan sun raba su da gidajensu

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane a Delta
'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane a jihar Delta Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Ƴan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane

Jami’in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Bright Edafe, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa an samu nasarar ne bayan kammala tattara bayanai kan wani mutum da aka sace a gidansa da ke Adjakota cikin ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a ranar, 17 ga watan Mayun 2024, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Daga baya masu garkuwa da mutanen sun kashe mutumin bayan sun yi garkuwa da shi.

An kashe ɗaya daga cikin masu garkuwa da mutanen a lokacin da sauran ƴan tawagarsa suka yi artabu da ƴan sanda.

Bright Edafe ya ce wanda ake zargin da ke boye a cikin daji ya samu munanan raunukan harbin bindiga kuma an kai shi asibiti inda daga baya ya mutu.

"Jami'an ƴan sandan ƙarƙashin jagorancin ASP Julius Robinson sun farmaki ɓata garin da suke da hannu a garkuwa da mutanen a ranar 1 ga watan Yulin 2024 inda suka cafke wani mai suna Ismaila Umaru mai shekara 28."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 4 a wani hari a jihar Katsina

"A ranar 4 ga watan Yulin 2024, wanda ake zargin ya jagoranci ƴan sanda wajen cafke sauran takwarorinsa su biyu masu suna Chede Mohammed mai shekara 18 da Mohammadu Sani mai shekara 26."
"Bisa bayanan da suka bayar, ƴan sanda sun dira maɓoyarsu da ke dajin Oviri-ogor a ranar 5 ga watan Yuli inda suka ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya."

- SP Bright Edafe

Karanta wasu labaran garkuwa da mutane

Ƴan bindiga sun sace manajan kamfani

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi garkuwa da manajan darakta na kamfanin Fouani mai wakiltar LG da Hisense a Legas.

Ƴan bindigan sun sace manajan ne tare da wasu ƴan kasar Lebanon guda uku a yayin da suke tafiya cikin kwale-kwale a Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng