Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'addan ISWAP 11 a Borno

Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'addan ISWAP 11 a Borno

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan mayaƙan ƙungiyar ƴan ta'addan ISWAP yayin wani artabu a jihar Borno
  • Sojojin tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai na CJTF sun hallaka ƴan ta'addan na ISWAP bayan sun kai samame a maɓoyarsu da ke cikin dajin Sambisa
  • Jami'an tsaron sun kuma yi nasarar ƙwato makamai masu yawa da suka haɗa da alburusai da bindigogi a maɓoyar ƴan ta'addan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan ƙungiyar ƴan ta'addan ISWAP guda 11 a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan ne a yankin Jongo da ke dajin Sambisa a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan tsige 'yan majalisa 25 da suka sauya bar PDP zuwa APC

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Borno
Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'addan ISWAP a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Sojoji sun hallaka ƴan ta'addan ISWAP

Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi ya ce dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan ne a ranar Juma'a, 5 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojojin tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai na CJTF, sun mamaye maɓoyar ƴan ta’addan ne a ranar 5 ga watan Yulin 2024.

Bayan samun nasarar hallaka ƴan ta'addan da sojojin suka yi, sun kuma ƙwato tarin makamai masu yawa daga maɓoyarsu.

Daga cikin makaman da suka ƙwato akwai harsasai guda 99 masu kaurin 7.62mm, da harsasai guda 19 na musamman masu kaurin 7.62mm, jigidar AK-4 guda uku, alburusai 47, bindigogi guda biyu da gurneti guda biyu.

Dakarun sojojin ba su samu asarar rai ko rauni ba yayin fafatawa da ƴan ta'addan, sai dai ɗaya daga cikin jami'an rundunar haɗin gwiwar ya samu rauni a yayin fafatawar.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun dakile harin 'yan ta'adda, sun kashe mutum 2 a Kaduna

Karanta wasu labaran kan ƴan ta'addan ISWAP

Ƴan ta'addan ISWAP sun hallaka masunta

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan ISWAP sun kashe masunta aƙalla 15 tare da jikkata wasu da dama a wani hari da suka kai a ƙaramar hukumar Kukawa a jihar Borno.

Ƴan ta'addan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 10:40 na dare, a lokacin da masunta ke shirin kamun kifi da daddare a yankin Tumbun Rogo Kangarwa da ke ƙaramar hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng