Samoa: Fitaccen Lauya Ya Yi Tsokaci Kan Yarjejeniya, Ya Ce Akwai Lauje Cikin Naɗi

Samoa: Fitaccen Lauya Ya Yi Tsokaci Kan Yarjejeniya, Ya Ce Akwai Lauje Cikin Naɗi

  • Fitaccen lauya a Najeriya ya yi magana kan yarjejeniyar Samoa inda ya ce akwai lauje cikin nadi game da tsare-tsaren
  • Lauyan mai suna Inibehe Effiong ya ce ya kamata gwamnati ta fito ta yi bayani dalla-dalla kan yarjejeniyar domin wayar da kan ƴan Najeriya
  • Effiong ya ce duba da sashen na 15 na yarjejejeniyar da ke kare hakkokin dan Adam musamman dangane da jinsi akwai rudani a ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake ta cece-kuce kan yarjejeniyar Samoa, babban lauya ya yi fashin baki kan lamarin.

Lauyan mai suna Inibehe Effiong ya yi fatali da yarjejeniyar inda ya ce akwai yaudara a cikin lamarin.

Kara karanta wannan

Lauya ta fayyace matsayar yarjejeniyar Samoa wajen kawo auren jinsi a Najeriya

Fitaccen lauya ya magantu kan yarjejeniyar Samoa a Najeriya
Lauya ya yi karin haske kan yarjejeniyar Samoa inda ya ce akwai yaudara a ciki. Hoto: @officialABAT/@DrDennisOuma.
Asali: Twitter

Samoa: Lauya ya fede gaskiya kan yarjejeniyar

Effiong ya bayyana haka ne a jiya Juma'a 5 ga watan Yulin 2024 inda ya ce rainin hankali ne a ce babu maganar auren jinsi a ciki, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan ya ce sashe na 15 na abubuwan da ke cikin tsarin suna haramta wariyar jinsi da siyasa da kuma wayar da kai kan jinsin ɗan Adam.

Ya ce hakan kuma ya kunshi auren jinsi wanda shi ne babban matsalar da yanzu ake korafi kanta a Najeriya.

Samoa: Lauya ya zargi yaudara a yarjejeniyar

"Sashe na 12 na kundin tsarin mulki ta shekarar 1999 ya ce babu wani yarjejeniya tsakanin Najeriya da wata ƙasa da zai zama doka har sai da sahalewar Majalisar Tarayya."
"Game da wannan yarjejeniya ta Samoa ya kamata Gwamnatin Tarayya ta fito wurin barranta kanta da wannan lamari."

Kara karanta wannan

Samoa: Bashir Aliyu Umar ya fadi matakin da majalisar shari’a za ta dauka kan gwamnati

"Amma duba da sashe na 15 na yarjejejeniyar akwai alamar tambaya tun da yana kare hakkin ɗan Adam ne bangaren jinsinsa."

- Inibehe Effiong

Samoa: Malamai sun dira kan Bola Tinubu

Kun ji cewa malaman addinin Musulunci da dama sun yi tsokaci kan yarjejeniyar Samoa da Gwamnatin Tarayya ta sanyawa hannu.

Malaman sun bayyana damuwa kan yarjejeniyar inda suka gargadi gwamnatin kan matsalolin da haka zai haifar a kasa.

Hakan ya biyo bayan sanya hannu a yarjejeniyar wanda Gwamnatin Tarayya ta ce ba shi da alaka da auren jinsi ko kadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.