Bidiyon Yadda Gwamna Bago Ya Umarci Dukan Malamin Musulunci a Zaman Makoki

Bidiyon Yadda Gwamna Bago Ya Umarci Dukan Malamin Musulunci a Zaman Makoki

  • Gwamna Umar Bago na jihar Niger ya nuna bacin ransa bayan wani ya yi kokarin yin addu'a a gidan mataimakin gwamnan jihar
  • Umar Bago ya umarci zabgawa malamin mari da kuma daukar mataki a kansa yayin zaman makokin a wani faifan bidiyo
  • Hakan ya biyo bayan bukatar a yi addu'a ga matar mataimakin gwamnan da ta rasu inda malamin ya so yin addu'a ba a bukace shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger - An shiga mamaki da al'ajabi bayan Gwamnan jihar Niger ya bukaci zabgawa malamin Musulunci mari.

Gwamna Umar Bago ya ba da umarnin ne yayin zaman makoki na rasuwar matar mataimakinsa a jihar.

Kara karanta wannan

Samoa: Bashir Aliyu Umar ya fadi matakin da majalisar shari’a za ta dauka kan gwamnati

Yadda Gwamna Bago ya umarci dukan malamin Musulunci a zaman makoki
Gwamnan Niger, ya nuna bacin ransa kan halin wani malamin Musulunci a zaman makoki. Hoto: Umar Mohammed Bago.
Asali: Facebook

Niger: Yadda Bago ya umarci marin malami

A wani faifan bidiyo da Daily Nigerian ta wallafa, an gano gwamnan na ba mai tsaronsa umarni ya mari malamin tare da kama shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya nuna bacin ransa bayan ya umarci wani ya yi addu'a sai malamin ya yi kokarin yi.

"Kai zan mare ka, kai malami ne? Ka mare shi, na ce ka mare shi sosai."
"Maza-maza ku kama shi, ku yi maganinsa sosai sannan ku dawo da shi."
"Ku shiga hankalinku ina da zuma kuma ina da madaci."

- Umar Bago

Niger: An yi addu'a ga marigayiya Zainab

Daga bisani gwamnan ya bukaci wani malami daban ya gudanar da addu'a ta musamman ga marigayiyar.

Lamarin ya faru ne a cikin gidan mataimakin gwamnan jihar bayan mutuwar matarsa, Hajiya Zainab Yakuba Garba.

Matar mataimakin Gwamna Bago ta rasu

Kara karanta wannan

"Da kun yi koyi da magabatanku": Farfesa ya shawarci Aminu Ado da Sanusi II

A wani labaron, kun ji cewa Allah ya yiwa uwargidan mataimakin gwamnan jihar Niger rasuwa.

Gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago ne ya bayyana hakan inda ya miƙa sakon ta'aziyyarsa tare da alhini kan rasuwar Hajiya Zainab Garba.

Sakon ta'aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mista Bologi Ibrahim, babban sakataren watsa labaran Gwamna Bago ya fitar a shafin gwamnatin jihar na X.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.