Sarautar Kano: Bidiyon Yadda Gidauniyar Dahiru Bauchi Ta Gudanar da Zikiri a Fadar Aminu Ado
- Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi ta gudanar da taron zikirin Juma'a da yammacin yau a fadar Nassarawa a Kano
- An gudanar da zikirin ne tare da gabatar da addu'o'i na musamman a fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero
- A jiya ne gidauniyar ta yi gayyata domin gudanar da zikirin ciki har da shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar Kano, an gudanar da zikirin Juma'a a fadar Nassarawa.
Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi ne ta shirya zikirin a fadar Sarkin Kano na 25, Aminu Ado Bayero a jihar.
An gudanar da zikiri a fadar Nassarawa
Masarautar Kano ta wallafa faifan bidiyon zikirin a yau Juma'a 5 ga watan Yulin 2024 inda aka yi addu'o'i na musamman.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi addu'o'i ne na musamman domin neman taimakon Ubangiji kan halin da kasar ke ciki a bangarori da dama.
A cikin bidiyon, an gano manyan baki wadanda suka cika fadar makil domin halartar taron zikirin.
Hakan ya biyo bayan shirya taron zikirin da Gidauniyar ta yi inda ya gayyaci Shugaba Bola Tinubu.
Iyalan Dahiru Bauchi sun ziyarci Aminu Ado
Wannan na zuwa ne bayan ziyarar mubaya'a da iyalan shehin malamin suka yi a fadar Aminu Ado a kwanakin baya.
Tawagar karkashin jagorancin Sayyadi Ibrahim Dahiru Bauchi ta gudanar da addu'o'i ga Aminu Ado.
Tun farko, wasu daga cikin ƴaƴan malamin karkashin jagorancin Aminu Dahiru Bauchi sun ziyarci fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Lauyoyin Aminu Ado sun janye daga shari'a
A wani labarin, kun ji cewa yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, lauyoyin Aminu Ado sun tsame jikinsu.
Lauyoyin sun janye ne a gaban Babbar Kotun jihar kan rashin jin dadinsu game da matakin da kotun ta dauka.
Barista Abdul Mohammed ya ce akwai matsaloli tattare da matakan da kotun ke dauka wanda ke kunshe da rashin adalci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng