Kano: Fusatattun Matasa Sun Fatattaki Wakilin Sanusi II Daga Karaye Bayan Cire Masu Sarki

Kano: Fusatattun Matasa Sun Fatattaki Wakilin Sanusi II Daga Karaye Bayan Cire Masu Sarki

  • Wakilin sarkin Kano na 16m Malam Muhammadu Sunusi II ya gamu da fushin wasu daga cikin mutanen kasar Karaye
  • Masarautar na daga masarautu biyar da sabuwar gwamnatin Kano ta rushe karkashin tsohon sarki Ibrahim Abubakar II
  • Wasu jami'in tsaro da ke zaune a kofar masarautar Karaye ne su ka kawo gudummawar korar fusatattun matasan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Wasu fusatattun matasa sun kori wakilin sarkin Kano na 16 Muhammadu Sunusi II daga karamar hukumar Karaye.

Matasan da sauran jama'ar gari sun bi wakilin sarkin da gudu da jifa har suka fasa gilashin motar da tawagarsa ke ciki.

Kara karanta wannan

An cafke uban da ya daure dansa mai shekaru 5 cikin sarka ya hana shi abinci

Kano map
Matasa sun kori wakilin sarkin Kano na 16 a Karaye Hoto: Legit Nigeria
Asali: Original

Daily Trust ta wallafa cewa lamarin ya afku ne lokacin da shugaban riko na karamar hukumar Karaye, Wada Nababa Tudun Kaya ke raka wakilin sarkin zuwa fadar masarautar yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karaye: Yan sandan Kano sun kawo dauki

Masarautar Karaye karkashin tsohon sarki Ibrahim Abubakar II na daga masarautun Kano biyar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta rushe. Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa wannan ne dalilin da ya sa matasan su ka kori wakilin sarki Muhammadu Sunusi II. Mutumin da ya nemi a sakaye sunansa ya ce jami'an 'yan sandan masarautar Karaye ne su ka kwantar da tarzomar.

An wulakanta wakilin Sarki a Karaye

"Abin da ya faru shi ne wakilin sarki ya shigo gari, sai kwantoman karamar hukuma ta tarbe shi. A hanyarsu ta zuwa fada ne, fusatattun matasa su ka farmake su."

Kara karanta wannan

Matashin da ya hallaka masallata a Kano ya amsa laifinsa, Kotu ta fitar da matsaya

- Shaidar gani da ido

Gwamnan Kano ya kori sababbin sarakuna

Tun bayan rushe masarautun jihar biyar, inda masarautun Gaya da Bauchi na ganin gwamnatin Kano ba ta kyauta masu ba.

Masarautar Bichi na ganin babu laifin da ta yiwa gwamnati da har ta kai ga yanke hukuncin rushe ta.

Sarki Sanusi II ya yaba wa gwamna Abba

A baya kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sunusi II ya yaba wa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa biyan hakkokin 'yan fansho.

Sanusi II ya kara da cewa muhimmin lamari ne yadda gwamnatin Kano waiwayi 'yan fansho da gwamnatin baya ta jefa cikin mawuyacin hali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.