N1.5b: Majalisa Ta Dakatar da Ayyuka a Ma’aikatar Mata, Ta Bukaci Minista Ta Gurfana

N1.5b: Majalisa Ta Dakatar da Ayyuka a Ma’aikatar Mata, Ta Bukaci Minista Ta Gurfana

  • Majalisar wakilai ta gayyaci ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta gurfana a gabanta cikin gaggawa
  • Yan majalisar sun gayyaci minista Uju Kennedy-Ohanenye ne bisa zargin wata badakalar kudi da ake zargi ta faru
  • Har ila yau, majalisar ta dauki matakin dakatar da gaba dayan ayyuka da ma'aikatar mata ta kasa ke yi a dukkan fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta bukaci ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta gurfana a gabanta.

Rahotanni sun nuna cewa majalisar ta gayyaci Uju Kennedy-Ohanenye ne bisa zargin badakala da ta faru a ma'aikatar mata.

Uju Kennedy-Ohaneye
An dakatar da ayyuka a ma'aikatar mata bisa badakala. Hoto Uju Kennedy-Ohanenye
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu daga cikin ma'aikatan da suke ma'aikatar mata sun yi bayani kan halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun tsige Mataimakin Shugaban kasa yana jinya a Kenya, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin gayyatar ministar mata

Majalisar wakilai ta bayyana cewa ta gayyaci ministar mata ne saboda zargin karkatar da kudi N1.5bn na yan kwangila.

Bincike ya nuna cewa yan kwangilar ne suka tura korafi ga majalisar bayan sun gama aiki ga ma'aikatar kuma ba a biya su ba, rahoton Leadership.

Karkatar da kudi: An zargi ministar mata

Shugabar kwamitin binciken, Kafilat Ogbara ta ce ma'aikatar mata ta fara wasu ayyuka da ba su cikin kasafin kudin shekarar 2023 bayan karkatar da N1.5bn.

Kafilat Ogbara ta kara da cewa ma'aikatar ta fara wasu ayyuka a jihohi 15 da sayen Keke NAPEP guda bakwai ga sojoji duk da cewa ana binta bashi.

Saboda haka majalisar ta bukaci dakatar da dukkan ayyukan da ma'aikatar ta fara har sai an samu bahasi kan yadda ma'aikatar ta kashe kudin da aka tura mata.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta dauki mataki bayan gano masu ɗaukar makamai, su aikawa miyagu

Ina kudin ma'aikatar mata suka shiga?

Daraktan kudi na ma'aikatar, Aloy Ifeakandu ya ce shi ma a shekarar 2023 ya fara aiki saboda haka ba zai ce komai ba kan abin da ya faru kafin zuwansa.

Sai dai ya ce yan kwangilar suna da takardun da suke rubuta dukkan abin da ya faru saboda haka a nemosu su yi bayani kan bashin da suke bi.

Majalisa ta gayyacci Wike

A wani rahoton, kun ji cewa bayan amsa gayyatar Majalisar Tarayya, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana gaskiyar kan garkuwa da mutane.

Wike ya ce babu wani yanki ko al’umma a fadin duniya da ba su fama da wani nau’i na rashin tsaro da yake addabarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng