Mahaifiyar Rarara Ta Rasa Ranta a Hannun 'Yan Bindiga? Gaskiya Ta Bayyana

Mahaifiyar Rarara Ta Rasa Ranta a Hannun 'Yan Bindiga? Gaskiya Ta Bayyana

  • Jaruma Aisha Humairah ta karyata rade-radin cewa mahaifiyar Dauda KahutuRarara ta rasa ranta a hannun masu garkuwa
  • Humairah ta bayyana haka ne yayin karin haske kan abin ake yadawa inda ta shawarci mutane su yi watsi da labarin
  • Jarumar ta ba da tabbata cewa da zaran Allah SWT ya kubutar da Mama za ta fito ta yi bayani kamar yadda ta saba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - An yi ta yaɗa rade-radin cewa mahaifiyar Dauda Kahutu Rarara ta rasa ranta a hannun masu garkuwa a kafofin sadarwa.

Sai dai Aisha Humairah ta karyata jita-jitar inda ta ce Mama, watau mahaifiyar Rarara tana nan cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

Borno: Majalisar dattawa ta faɗi sakacin da ya jawo aka kai harin bam a Gwoza

An bayyana gaskiya kan rasuwar mahaifiyar Rarara a hannun 'yan bindiga
Aisha Humairah ta karyata labarin rasuwar mahaifiyar Rarara. Hoto: Dauda Kahutu Rarara.
Asali: Facebook

An gano gaskiya kan rasuwar mahaifiyar Rarara

Aisha ta bayyana haka a yau bayan sallar Juma'a a faifan bidiyon TikTok inda ta yi godiya ga masu taya su addu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jarumar ta ce duk lokacin da aka sako Mama za ta sanar da al'umma kamar yadda take yi inda ta roki mutane su bar yada jita-jita.

Wannan na zuwa ne bayan wasu sun yi ta yaɗa rade-radin cewa mahaifiyar mawakin ta rasu a hannun ƴan bindiga.

Rarara: 'Yan bindiga sun bukaci N900m

Dattijuwar ta shafe mako guda kenan a hannun ƴan bindiga inda suka bukaci kudin fansa har N900m.

Wata majiya ta bayyana cewa tun da farko ƴan bindigan da suka sace mahaifiyar Rarara sun kira waya inda suka buƙaci a biya su N1bn a matsayin kuɗin fansa.

'Yan bindiga sun sace mahaifiyar Rarara

Kara karanta wannan

Malamin addini ya rasa ransa bayan ɗansa ya yi sanadiyyar ajalinsa yana bacci

A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai hari Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja, sun yi garkuwa da mahifiyar Dauda Kahutu Rarara.

Mun samu rahoton da safiyar ranar Jumu'a 28 ga watan Yulin 2024 inda maharan suka ɗauki mahaifiyar fitaccen mawakin a kauyen Kahutu da ke jihar Katsina.

Daga bisani 'yan sanda sun tabbatar da kama wasu mutane da ake zargin da hannunsu a satar dattijuwar inda suka kaddamar da bincike.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel