NNPP Ta Tsame Kanta Daga Aikawa 'Yan Majalisa Wasika Kan Rikicin Sarautar Kano

NNPP Ta Tsame Kanta Daga Aikawa 'Yan Majalisa Wasika Kan Rikicin Sarautar Kano

  • Ana ci gaba da rikicin masarautar Kano, sai aka jiyo jam'iyyar NNPP ta bayyana cewa matsalar cikin gida ce da bai kamata ta tsoma baki ba
  • Shugaban jam'iyyar na kasa, Dr. Major Agbo ne ya bayyana haka lokacin da ya ke martani kana wata wasika ga majalisa kan rikicin
  • Dr. Major Agbo ya kara da cewa a matsayinsu na jam'iyya, bai kamata su ce wani abu kan dambarwar masarautar ba duk da NNPP ke mulki a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Uwar jam'iyyar NNPP ta musanta wata wasika da aka rubuta ga 'yan majalisa kan rikicin masarautar Kano.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: NNPP ta yi hannun riga da Kwankwaso kan zargin tasa Tinubu a gaba

Shugaban jam'iyyar na kasa, Dr. Major Agbo ne ya barranta NNPP da wasikar ta cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Masarauta
NNPP ta raba kanta da wasika ga majalisa kan rikicin masarauta Hoto: Sanusi Lamido/Nigerian Senate/Masarautar Kano
Asali: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa Dr Major Agbo ya ce a matsayinsu na jam'iyyar siyasa, babu ruwansu da dambarwar masarautar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Rikicin sarauta matsalar cikin gida ce" - NNPP

Wani Dr. Ajuji Ahmed ya rubuta wasika ga majalisar dattawa ya na neman 'yan majalisar NNPP su dauki matakin kawo karshen katsalandan din gwamnatin Tinubu cikin rikicin masarautar Kano.

Amma a martanin da shugaban jam'iyyar, Dr. Major Agbo ya fitar, ya ce Dr. Ajuju Ahmed sojan gona ne, saboda haka majalisa ta sa a kama shi.

Ya kara da cewa rikicin masarautu a Kano lamari ne na cikin gida, saboda haka a matsayin NNPP na jam'iyyar, babu ruwanta a ciki, kamar yadda aka wallafa.

Kara karanta wannan

"Muna tsoron faruwar irin zanga-zangar Kenya": Jigon APC ya gargadi Tinubu

Shugaban ya shawarci gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da dattijon kasa, Buba Galadima cewa dole ne a bi hukuncin kotu kan rikicin.

Rikicin sarauta: Kwankwaso ya rubuta wasika

A baya mun ruwaito cewa an gano wata wasika da dan takarar shugaban kasa a NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso ya rubuta zuwa ga 'yan majalisar jam'iyyar.

Kungiyar Progressive League of Youth Voters ta zargi Sanata Kwankwaso da rubuta wasikar ya na bukatar 'yan majalisar su caccaki shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.