Yan Sanda Sun Yi Musayar Wuta da ’Yan Ta’adda, an Kashe Yan Bindiga 9
- Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Legas ta samu nasara kan wasu gungun yan ta'addan da suka addabi jihar da kai hare hare
- Rahotanni sun nuna cewa rundunar ta fafata da yan ta'addar ne kaifin daga bisani su samu nasarar murƙushe su baki daya
- Har ila yau, rundunar yan sandan ta samu nasarar kwace wasu makamai da yan ta'addar ke aiki da su wajen kai hare hare a fadin jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Legas ta yi nasarar kashe wasu miyagu yan bindiga.
Rahotanni sun nuna cewa jami'an yan sanda sun yi musayar wuta da miyagun kafin samun nasara a kansu.
Jami'an yan sanda sun tabbatar wa gidan talabijin din Channels cewa jami'ansu na musamman ne suka fafata da yan bindigar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan bindiga nawa aka kashe a Legas?
Rahotanni sun nuna cewa rundunar yan sanda ta kashe gungun yan bindiga tara ne yayin da suka yi musayar wuta.
Har ila yau, an fafata tsakanin yan sanda da miyagun ne a yankunan Isolo, Ajao, Okoto, da Ladipo a jihar ta Legas.
Me aka kwato hannun yan bindigar?
Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa ta kwato bindigogi ƙirar AK47 guda biyar a wajen yan ta'addar.
Haka zalika rundunar ta samu nasarar kwace mota kirar SUV daga hannun yan bindigar bayan sun fafata.
Yan sanda sun ceto budurwa a Legas
Rundunar yan sanda a jihar Legas ta wallafa a Facebook cewa ta ceto wata budurwa mai shekaru 19 daga aikata kisan kai.
Budurwar wacce ba a bayyana sunanta ba ta fadi cewa ta yi nufin kashe kanta ne bayan damuwar duniya ta mata yawa.
Yan sanda sun kama tabar wiwi a Legas
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandar jihar Lagos ta sanar da kama wani mutum dauke da buhunan tabar wiwi guda 30 a Ojo.
Rahotanni sun nuna cewa mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin yace sun kama mutumin ne da asuba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng