'Yan Bindiga Sun Saki Alkalin Kotun Kaduna Amma Sun Rike ’Ya’yanta 4, Suna Neman N150m
- Wata alƙalin kotun gargajiya, Janet Gimba da ke jihar Kaduna ta shaƙi iskar 'yanci bayan sace ta da 'yan bindiga suka yi
- An ruwaito cewa wadanda suka sace ta sun sake ta yayin da suka ci gaba da riƙe 'ya'yanta duk da cewa sun halaka daya a cikinsu
- Yanzu haka dai an ce suna neman Naira miliyan 150 matsayin kudin fansa kafin su sako yaran, kuma sun ba da wa'adin kwana shida
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Mai shari'a Janet Gimba, alƙali a kotun gargajiya da ke Kaduna, wacce aka yi garkuwa da ita tare da 'ya'yanta a watan Yuni, ta samu 'yanci.
An ce har yanzu 'ya'yanta suna hannun waɗanda suka yi garkuwa da su bayan da aka gano cewa sun kashe ɗaya daga ciki mai shekaru 14, mai suna Victor.
'Yan bindiga na neman N150m
Wannan lamarin ya matuƙar girgiza jama'a sakamakon rashin tausayin da 'yan bindigan suka nuna ƙarara, kamar yadda rahoton Daily Trust ya bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dr. Musa Gimba, mijin alƙalin ya tabbatar da sakin matarsa amma ya bayyana cewa har yanzu waɗanda suka yi garkuwa da su na buƙatar Naira miliyan 150 kafin su sako yaran.
Ya ce masu garkuwar sun bayar da wa'adi, inda suke buƙatar kuɗin fansar cikin kwanaki shida daga ranar Laraba kuma sun yi barazanar cutar da sauran yaran.
Rundunar 'yan sanda tayi bayani
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da sakin alƙalin da kuma kisan Victor ga manema labarai.
Kakakin rundunar a Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya tabbatarwa da jama'a cewa hukumomi suna aiki ba dare ba rana domin ceto sauran waɗanda aka yi garkuwa dasu.
Ya ce jami'ai sun samu gawar Victor a Ungwan Bayero, kauyen Dutse, kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Talata, 2 ga Yulin 2024.
'Yan gari sun ragargaji 'yan bindiga
A wani labari na daban, mazauna jihar Kaduna sun fara gundura da lamarin 'yan bindiga inda wasu zaƙaƙurai suka fatattake miyagun a lokacin da suka kai hari.
Wannan lamarin ya faru ne a ƙauyen rugar Sojidi da ke ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, kuma an ce mazauna garin sun jaddada kudurin cigaba da kare kansu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng