Sarautar Kano: Lauyoyi Sun Bayyana Dalilin Janye Jiki Su Bar Shari'ar Aminu Ado a Kotu
- Lauyoyin da ke kare Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero sun janye daga shari'ar da ake yi kan wasu zarge-zarge
- Lauyoyin sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda kotun na Kano ke daukar matakai da ba su hango adalci a ciki ba
- Hakan ya biyo bayan ci gaba da dambarwa kan rigimar sarautar da ake ciki tun a watan Mayun 2024 da ta gabata
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, lauyoyin Aminu Ado sun tsame jikinsu.
Lauyoyin sun janye ne a gaban Babbar Kotun jihar kan rashin jin dadinsu game da matakin da kotun ta dauka.
Lauyoyin Aminu Ado sun bar shari'ar Kano
Barista Abdul Mohammed ya ce akwai matsaloli tattare da matakan da kotun ke dauka wanda ke kunshe da rashin adalci, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan ya ce ya bukaci kotun ta dage ci gaba da sauraran shari'ar amma ta ki ba su dama wanda hakan ya sake nuna akwai rashin gaskiya.
Daga bisani, Mohammed ya janye daga ci gaba da kasancewa a matsayin lauyan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, Vanguard ta tattaro.
Har ila yau, Barista Sanusi Musa a madadin sauran lauyoyin shi ma ya janye daga kare Aminu Ado.
Kano: Korafin da aka shigar a kotu
Masu korafi a gaban kotun sun hada da kwamishinan shari'a na jihar Kano da kakakin Majalisar jihar.
Sai kuma Majalisar jihar da kanta wanda lauyansu Ibrahim Isah Wangida ya shigar da korafi a ranar 27 ga watan Yulin 2024.
Masu korafin suna neman kotun ta dakatar da Aminu Ado da sauran sarakuna hudu da aka tsige ci gaba kiran kansu masu sarauta.
Sarakuna guda hudun sun hada da na garuruwan Bichi da Karaye da Gaya da kuma Rano.
Kotu ta dage sauraron shari'ar sarautar Kano
Kun ji cewa Babbar Kotun jihar Kano da ke sauraron shari'ar sarauta ta yi zama kan rigimar inda ta dauki mataki a wannan mako.
Kotun ta dage ci gaba sauraron shari'ar har zuwa ranar yau Alhamis 4 ga watan Yulin 2024 domin daukar matakin gaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng