'Yan Sandan Kano Sun Cafke 'Yan bindiga da 'Yan Daba Sama da 100 Cikin Kwanaki 10
- Rundunar yan sandan Kano ta samu nasarar tattaro masu aikata miyagun laifuffuka a loko da sakon da ke cikin jihar
- A cikin kwanaki 10, 'yan sanda sun hado kan bata-gari kimanin 149 da suka addabi mazauna jihar da mugun aiki
- Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an kama har da masu garkuwa da mutane
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasarar kan masu aikin ta'addanci a jihar.
Rundunar ta yi holin matasa akalla 149 da aka kamo daga cikin loko da sakunan Kano a tsakanin kwanaki 10, dai-dai. da kwanakin fara aikin sabon kwamishinan yan sanda a jihar.
A sakon da jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, 'yan daba sun fi yawa cikin wadanda aka kama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama 'yan daba 106 a jihar Kano
Yayin da fadan daba ke kokarin mamaye wasu yankunan dage birnin Kano, 'yan sanda sun kama 'yan daba 106 cikin kwanaki 10.
The Nation ta wallafa cewa sauran wadanda aka kama sun hada da 'yan fashi 25, masu garkuwa da mutane biyu da masu sayar da miyagun kwayoyi uku.
An kwace makaman miyagu a Kano
Rundunar yan sandan Kano ta kwace mugayen makamai daga hannun bata-garin da ta kama kwanaki 10 da suka wuce.
Daga cikin makaman da aka kwace akwai bindigogi, wukake 58, kwari-da-baka da adduna.
An kuma kama babura masu kafa biyu da masu kafa uku, sai tarin miyagun kwayoyi ciki har da wiwi da sholisho.
'Yan daba sun yunkura kai hari Kano
A wani labarin kun ji cewa wasu gungun 'yan daba sun yi kokarin tarwatsa bikin rantsar da ke kwamishinoni a fadar gwamnatin Kano.
Sai dai rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana samun nasarar damke 'yan dabam da ake zargi tare da dakile yunkurin tayar da zaune tsaye a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng