Dakarun Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Ta'adda, Sun Hallaka Mutum 2 a Kaduna

Dakarun Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Ta'adda, Sun Hallaka Mutum 2 a Kaduna

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar rage mugun iri bayan sun yiwa ƴan ta'adda da ke kan hanayar kai hari kwanton ɓauna a jihar Kaduna
  • Sojojin sun yi nasarar hallaka ƴan ta'adda mutum biyu yayin da suka yi musayar wuta a ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar
  • Bayan hallaka ƴan ta'addan guda biyu, sojojin sun kuma ƙwato makamai masu yawa daga ƴan ta'addan masu tayar da ƙayar baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta da ke yaƙi da ta'addanci a jihar Kaduna, sun yi nasarar daƙile wani harin ƴan ta'adda.

Rundunar ta ce dakarun sun kuma yi nasarar hallaka ƴan ta'adda mutum biyu bayan sun yi musu kwanton ɓauna.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace alkaliya da 'ya'yanta 4, sun bukaci a ba su N300m

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Kaduna
Sojojin Najeriya sun hallaka 'yan ta'adda a jihar Kaduna Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da rundunar sojojin Najeriya ta sanya a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda a Kaduna

Sanarwar ta bayyana cewa sojojin bayan samun bayanin sirri sun yiwa ƴan ta'adda huɗu da ke kan babura kwanton ɓauna a Kurmin Aja, cikin ƙaramar hukumar Kagarko yayin da suke kan hanyar kai hari.

Dakarun sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta'addan tare da hallaka biyu daga cikinsu yayin da sauran suka tsere ɗauke da raunukan bindiga zuwa cikin daji.

Bayan artabun da ƴan ta'addan, sojojin sun kuma ƙwato makaman da suka haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, harsasai guda 30 masu kaurin 7.62mm, jigida guda uku da babura guda biyu.

Rundunar sojojin ta shawarci mutanen yankin da su kasance masu sanya ido kan abubuwan da ke faruwa, su ci gaba da gudanar harkokinsu na yau da kullum tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 4 a wani hari a jihar Katsina

Dakarun sojoji sun sheƙe ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun runduna ta ɗaya ta sojojin Najeriya da ke aiki a Kaduna sun kashe ƴan ta'adda bakwai a ƙauyen Udawa da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar.

Dakarun sojojin sun samu nasarar ne a wani aikin sintiri da suka gudanar a kan hanyar Udawa-Kurebe a ranar Lahadi, 19 ga watan Mayun 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel