'Yan Bindiga Sun Sace Alkaliya da 'Ya'yanta 4, Sun Bukaci a Ba Su N300m

'Yan Bindiga Sun Sace Alkaliya da 'Ya'yanta 4, Sun Bukaci a Ba Su N300m

  • Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da wata alƙaliya tare da ƴaƴanta huɗu a jihar Kaduna sun buƙaci a ba su N300m a matsayin kuɗin fansa
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka babban ɗanta bayan an kasa biyan kuɗaɗen da suka nema tare da barazanar hallaka sauran
  • Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa tana bakin ƙoƙarinta domin ganin ta ceto su daga hannun ƴan bindigan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wata alƙaliyar kotu, Janet Galadima-Gimba, tare da ƴaƴanta maza huɗu a Kaduna.

Rahotanni sun ce ƴan bindigan sun sace alƙaliyar da ƴaƴanta a gidansu da ke unguwar Mahuta a Kaduna a ranar 23 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka 'yan gudun hijira bayan sun raba su da gidajensu

'Yan bindiga sun sace alkaliya a Kaduna
'Yan bindiga sun bukaci a ba su N300m bayan sace alkaliya a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Kaduna

Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da su, waɗanda adadinsu ya kai 15, sun kai farmaki gidan ne da daddare a lokacin da mijinta wanda likita ne, yake wajen aiki, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindigan sun buƙaci da a ba su N300m matsayin kuɗin fansa kafin su sake su tare da yin barazanar hallaka su idan aka kasa biyan kuɗaɗen.

Da take mayar da martani kan hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, shugabar ƙungiyar 'House of Justice', Gloria Ballason, ta yi kira da a kare alƙaliyar tare da iyalanta.

Gloria Ballason ta ce masu garkuwa da mutanen sun kashe babban ɗan alƙaliyar mai shekaru 14 bayan da iyalan suka kasa biyan kuɗin fansan da suka nema.

Ta ce yaron mai suna Victor Gimba, an harbe shi ne a ranar 2 ga watan Yulin 2024, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 4 a wani hari a jihar Katsina

"Ƴan bindigan waɗanda sun kai kimanin mutum 15, sun yi garkuwa da su, kuma sun nemi maƙudan kuɗaɗe a matsayin kuɗin fansa."
"A ranar Talata, 2 ga watan Yuli, 2024, ƴan bindigan sun harbe Victor Gimba, wanda shi ne babban ɗa a wajen alƙaliyar bayan an kasa biyan kuɗin fansan."

- Gloria Ballason

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ya tabbatar da faruwar lamarin.

Mansur Hassan ya ce rundunar tana yin iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin an ceto mutanen.

Batun harin bam a hanyar Abuja-Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta yi watsi da rahotannin da ke cewa an kai harin ƙunar baƙin wake a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Laraba.

Musanta kai harin ƙunar baƙin waken na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar.

Kara karanta wannan

'Yan bindigan da suka sace mahaifiyar Rarara sun fadi kudin fansan da za a biya su

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel