Auren Jinsi: An Soki Gwamnatin Tarayya Kan Sanya Hannu a Yarjejeniyar $150bn Ta Samoa
- Ana ta ce-ce-ku-ce a Najeriya kan yarjejeniyar Samoa da Gwamnatin Tarayya ta shiga wanda ake zargin akwai auren jinsi a ciki
- A ranar 1 ga watan Yulin 2024, Ministan Kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya rattaba hannu a yarjejeniyar Samoa na $150bn
- Sai dai kakakin Ministan, Bolaji Adebiyi ya ce yarjejeniyar da aka sanyawa hannu ta inganta kasuwanci da tattalin arziki ce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Wasu malaman addini da kungiyoyin fafutuka sun fusata kan sanya hannu a yarjejeniyar samoa.
Akwai abubuwa da dama a kunshe a cikin tsarin Samoa wanda ya haɗa da auren jinsi da sauran bangarori na ci gaban al'umma.
Tsare-tsaren da yarjejeniyar Samoa ta kunsa
Kasashen da suka ci gaba suna tilasta wasu masu tasowa amincewa da Samoa domin samun tallafi ko basuka na kudi, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu rahoton rattaba hannun ne a ranar 1 ga watan Yulin 2024 bayan Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya tabbatar da haka.
Najeriya ta shiga yarjejeniyar auren jinsin SAMOA?
Hadimin Ministan, Bolaji Adebiyi ya tabbatar da cewa an sanya hannun ne a bangaren ci gaban tattalin arziki kadai daga cikin tsarin Samoa, New Telegraph ta tattaro.
Adebiyi ya ce babu inda aka yi maganar auren jinsi a cikin yarjejeniyar da suka sanyawa hannu inda ya ce bai kamata a yi zargin haka ba.
Samoa: Bangaren yarjejeniyar da aka sanya hannu
Ya ce Bagudu ya sanya hannu ne a yarjejeniyar tattalin arzikin $150bn domin haɓaka kasuwanci da inganta rayuwar al'umma.
Da aka tuntubi kakakin Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi mai suna Kamarudeen Ogundele ya ce zai yi bincike kan lamarin kafin yin martani.
Legit Hausa ta ji ta bakin wani mai fashin baki kan wannan yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya sanyawa hannu.
Ali M. Ali ya ce wannan shi ne sakamakon zaben tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi a Najeriya.
Ya ce kadan ma aka gani amma ya kamata malamai da suka tallata Tinubu su fito su yi magana.
Sai dai shugaban wata kungiyar matasa, Kwamred Umar Lastdon ya ce mutane ba su fahimci tsarin da ke cikin Samoa ba.
Umar ya ce ya kamata gwamnati ta fito ta yi karin haske saboda fayyace abubuwan da ke cikin yarjejeniyar ga ƴan ƙasa.
Dan Majalisa ya magantu kan yarjejeniyar Samoa
Kun ji cewa Dan Majalisar Wakilai a mazabar Sumaila/Takai a Kano, Rabiu Yusuf ya ce Najeriya na iya amincewa da sassa masu kyau na yarjejeniyar Samoa.
Hon. Yusuf ya ce yarjejeniyar ta kasance mai wahala da za a iya tattaunawa a kai saboda tana kunshe da wani bangare na mutunta 'yancin auren jinsi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng