Rigimar Sarauta: Farfesa a Kano Ya Zargi Kwankwaso da Saka Siyasa Tun Farkon Lamarin

Rigimar Sarauta: Farfesa a Kano Ya Zargi Kwankwaso da Saka Siyasa Tun Farkon Lamarin

  • Farfesa a Jam'iar Yusuf Maitama Sule ya yi tsokaci kan yadda siyasa ta shiga lamarin rigimar sarautar Kano
  • Farfesa Umar Labdo ya ce Rabiu Kwankwaso ya nada Muhammadu Sanusi II ne tun a 2014 saboda gabar siyasa
  • Labdo ya ce idan ba a yi hankali ba rigimar za ta farraka iyalan da suke da alaka da juna da kuma jawo rikici Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, Farfesa Umar Labdo ya bayyana musabbabin rikicin.

Farfesan wanda ke koyarwa a Jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke jihar Kano ya ce siyasa ce ta jawo wannan rigima tun asali.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: NNPP ta yi hannun riga da Kwankwaso kan zargin tasa Tinubu a gaba

Farfesa ya bayyana yadda Kwankwaso ya saka siyasa a rigimar sarautar Kano
Farfesa Umar Labdo ya ce Rabiu Kwankwaso ya nada Sanusi II ne a 2014 saboda siyasa. Hoto: Chris Adetayo, Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Facebook

An zargi Kwankwaso da siyasantar da sarauta

Farfesa Labdo ya bayyana haka yayin hira da jaridar Vanguard inda ya fadi dalilin nada Muhammadu Sanusi tun farko a 2014.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesan ya ce Rabiu Kwankwaso ya nada Sanusi II saboda ya batawa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan rai bayan ya kori sarkin daga gwamnan bankin CBN.

Ya ce tsan-tsar siyasa ce ta jawo nadin domin batawa Jonathan rai saboda matakin da ya dauka kan Sanusi II.

Farfesan ya ce siyasa ta taka rawa

"Wannan rigima siyasa ce kawai da kuma kulle-kullen 'yan siyasa, Rabiu Kwankwaso ya nada Sanusi a 2014 a mulkin Goodluck Jonathan domin siyasa."
"Mutane da dama sun yi imanin cewa an yi hakan ne domin batawa Jonathan rai wanda a lokacin bai shiri da Sanusi."
"Daga bisani, Abdullahi Ganduje ya tube shi tare da nada Aminu Ado Bayero, wannan tsan-tsar siyasa kenan, sannan Abba Kabir ya dawo da Sanusi."

Kara karanta wannan

An shiga jimamin mutuwar wata Farfesa cikin wani yanayi maras dadi a gidanta a Maiduguri

- Farfesa Umar Labdo

Sarautar Kano: Farfesa Labdo ya yi gargadi

Farfesan ya nuna takaici yadda siyasa ta shiga da neman kawo rigima da gaba a tsakanin iyalai inda ya ce hakan zai iya jawo fitina a Kano.

Ya ce siyasa muguwar wasa ce idan ba a yi hankali za ta ruguza ba iya Kano ba har ma da Arewacin Najeriya.

Kotu da dage sauraron shari'ar sarautar Kano

Kun ji cewa a zaman Babbar kotun jiha da aka yi an dauki matakin dage sauraron karar zuwa gobe Alhamis 4 ga watan Yulin 2024.

Kotu ta dauki matakin ne yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar tsakanin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel