Gwamna Ya Sanya Dokar Zaman Gida Ta Tsawon Sa'o'i 24 a Ƙaramar Hukumar Ukum

Gwamna Ya Sanya Dokar Zaman Gida Ta Tsawon Sa'o'i 24 a Ƙaramar Hukumar Ukum

  • Gwamna Hyacinth Alia ya sanya dokar zaman gida a karamar hukumar Ukum da kewayenta biyo bayan zanga-zangar da ta ɓarke
  • Matasa sun ɓarke da zanga-zanga a Sankera, hedkwatar da ƙaramar hukumar Ukum ne sakamakon kisan mutane 11 a yankin
  • Gwamna Alia ya ce dokar za ta fara aiki daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa ƙarfe 6:00 na safiya daga gobe Alhamis, 4 ga watan Yuli

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai a ranar Laraba ya sanya dokar zaman gida ta tsawon sa'o'i 24 a karamar hukumar Ukum da ke jihar.

Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne sakamakon zanga-zangar da ta ɓalle a Sankera, hedkwatar ƙaramar hukumar Ukum da safiyar ranar Laraba, 3 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Fusatattun matasa sun bankawa ofishin INEC wuta, bayanai sun fito

Gwamna Hyacinth Alia.
Gwamnatin Benue ta sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a karamar hukumar Ukum Hoto: Rev. Hyacinth Alia
Asali: Facebook

Menene ya kawo zanga-zanga a Ukum?

Matasa sun ɓarke da zanga-zanga ne biyo bayan kisan mutane 11 da mahara suka yi a yankin, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu zanga-zangar sun farmaki sakatariyar ƙaramar hukumar kuma sun lashi takobin za su ƙona ta domin nuna takaicinsu da kashe ƴan uwansu.

Sun kuma ɗauki gawarwakin waɗanda aka kashe sun jera su a wurin ajiye motar shugaban ƙaramar hukuma, Victor Iorzaa.

Tun da farko Mista Iorzaa ya shaidawa manema labarai a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai cewa ba zai iya cewa komai ba kan lamarin.

Benue: Gwamna ya sa dokar kulle

Gwamna Alia ya sanar da sanya dokar kulle ne ta hannun mataimakin gwamna, Barista Sam Ode, kamar yadda PM News ta tattaro.

“Daga yau 3 ga Yuli, 2024, mun kafa dokar hana fita a karamar hukumar Ukum da kewaye.

Kara karanta wannan

An samu asarar rayuka a rikicin manoma da makiya a jihar Jigawa

"Dokar za ta fara aiki ne daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe daga gobe 4 ga watan Yuli 2024 har sai baba ta gani,”

- Sam Ode

Ana sa ran samun tsaro a Ukum

Alia ya kuma yi kira da a kwantar da hankula, inda ya ce an tura jami’an tsaro domin wanzar da zaman lafiya a Ukum musamman yankin Sankera.

Ana fama da kashe-kashe a Binuwai musamman a 'yan kwanakin bayan-bayan nan.

Majalisa ta yi magana kan harin Gwoza

A wani rahoton na daban majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ta umarci sojoji su sauya salon yaƙi da ƴan tada kayar baya a Najeriya.

A zaman ranar Laraba, 3 ga watan Yuli, majalisar ta ɗora alhakin harin bam da aka kai a Gwoza kan sakacin tattara bayanan sirri.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262