Majalisa ta Hango Matsala, Sanatoci Sun Koka Kan Shigo da Gurbataccen Mai a Najeriya
- Yan majalisar dattawan Najeriya sun shiga fargabar yadda aka samu bazuwar gurbataccen man fetur da na dizel kasuwannin kasar nan
- A zaman majalisar na ranar Laraba, an bayyana yadda ake zargin an kai lalataccen man da ya kai tan 660 domin sayar da su kasashen Afrika
- Sanata Asuquo Ekpeyong ya shaidawa majalisa cewa ana sa ran sayar da duk yawan fetur din mara kyau ne a kasuwannin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Majalisar Dattawa ta ankarar da yan kasar nan cewa an shigo da wani nau'in gurbataccen man fetur da kuma dizel cikin kasar.
Sanata Asuquo Ekpeyong ya shaidawa majalisa cewa ranar 16 ga watan Yunin 2024 wani rahoto ya nuna cewa wasu jiragen dakon kaya 12 sun kai tan 660 na man dizel zuwa birnin Lome na Togo.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa za a sayar da fetur da dizel ɗin ne a kasuwannin kasashen Afirka ta yamma, musamman Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kafa kwamitin binciken man fetur
Sanata Asuquo Ekpeyong ya ce ingancin man bai kai na wanda aka saba amfani da shi a kasar ba kamar yadda Channels Television ta wallafa.
Ya bayyana fargabar cewa amfani da gurbataccen fetur din zai iya haifar da matsala ga ababen hawan yan kasar nan.
Majalisar ta amince da kafa kwamitin gaggawa domin ya bincika man da ake shigowa da shi, wanda suka ce yana da hadari matuka ga yan kasa.
NMDPRA ta na ina ake shigo da fetur?
Ya ce sanin kowa ne hukumar kula da hakowa da cinikin man fetur ta NMDPRA ta sauya dokokin nau'in man da ake amfani da shi kamar yadda sabuwar dokar man fetur ta tanada.
Amma ana ganin kawo yanzu, hukumar ba ta iya saka ido kan amfani da man a fadin kasar nan.
An sanya dokar ta baci kan hako fetur
A baya mun kawo labarin cewa kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya bayyana dokar ta baci kan hako man fetur a Najeriya.
Haka kuma gwamnatin tarayya ta yi watsi da zargin da kamfanin man Dangote ya yi na cewa ana shigowa da gurbataccen man fetur kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng