Sanatocin Kudu Maso Gabas Sun Gana da Ministan Shari'a Domin a Saki Nnamdi Kanu

Sanatocin Kudu Maso Gabas Sun Gana da Ministan Shari'a Domin a Saki Nnamdi Kanu

  • Sanatocin Kudu maso Gabas a kasar nan sun hada kansu tare da neman gwamnatin Najeriya ta saki shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu
  • Enyinnaya Abaribe mai wakiltar Abia ta Kudu ne ya ja tawagar, inda ya ke ganin sakin Kanu zai kawo kwanciyar hankali
  • Sun gana da babban lauyan kasa, Lateef Fagbemi SAN a dai-dai lokacin da gwamnonin Kudu maso Gabas ke kokarin ganawa da shugaba Tinubu kan batun

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Sanatoci daga Kudu maso gabashin kasar nan sun gana da babban lauyan kasa kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi SAN kan batun shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta yiwa wasu 'yan Najeriya gata, an dakatar da karbar haraji daga garesu

A ganawar da su ka yi, sanatocin sun nemi gwamnatin tarayya ta saki Nnamdi Kanu da ke tsare a halin yanzu saboda zargin cin amanar kasa da wasu tuhume-tuhumen.

Nigerian Senate
Sanatocin Kudu maso Gabas sun nemi a saki shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Sanatoci akalla 15 ne su ka gana da babban lauyan bisa jagorancin dan majalisa mai wakiltar Abia ta Kudu, Enyinnaya Abaribe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tsare Kanu na jawo rashin tsaro," Sanatoci

Jaridar This day ta wallafa cewa sanatocin kudu maso gabashin Najeriya sun bayyana cewa ci gaba da tsare shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu na jawo matsala.

Sanatocin da suka ziyarci babban lauyan kasa kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi SAN sun ce ci gaba da tsare Mista Kanu na jawo karuwar rashin tsaro a yankinsu.

Sanata Enyinnaya Abaribe da ya jagoranci tafiyar ya ce su na fatan Fagbemi SAN zai taushi shugaban kasa Bola Tinubu domin sakin Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

"A koma salon mulkinsu Sardauna": An fadawa Tinubu hanyar magance matsalolin Najeriya

Sanatocin sun bayyana rashin jin dadin yadda wasu suka mayar da bukatar sakin Kanu wata hanya ta kashe-kashe a yankunansu.

Gwamnoni sun nemi a saki Nnamdi Kanu

A baya mun kawo labarin cewa gwamnonin jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya sun tattauna a garin Enugu inda suka hade kai wajen neman shugaba Tinubu ya saki Nnamdi Kanu.

Gwamnatin tarayya na shari'a da Nnamdi Kanu saboda zarginsa da cin amanar kasa da fafutukar ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Biafra, wanda hakan ke jawo asarar rayuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel