An Bankado Yadda Sambo Dasuki Ya Ba Tsohon Gwamna N1.2bn Daga Kudin Makamai
- Mai ba da shaida kuma mai bincike a hukumar EFCC ya ba da shaidar yadda Sambo Dasuki ya tura makudan kudi ga tsohon gwamna
- Abubakar Madaki ya ce Dasuki ya tura kudi har N1.2bn ga Ayo Fayose domin batar da inda asali kudin suka fito da ake zargi na makamai ne
- Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da binciken tsohon gwamnan na jihar Ekiti, Fayose kan badakalar N6.9bn lokacin mulkinsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Yayin da ake ci gaba da shari'ar tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, an bankado wata badaƙala.
Wani mai ba da shaida a kotu ya bayyana yadda tsohon mai ba da shawara a harkokin tsaro, Sambo Dasuka ya ba Fayose N1.2bn.
EFCC: An gano badakalar Dasuki da Fayose
Abubakar Madaki, mai bincike a EFCC ya fadawa alkalin kotun, Chukwujekwu Aneke cewa Dasuki ya ba Fayose kudin domin batar da ainihin tushensu, cewar hukumar EFCC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tuhumar tsohon gwamna Fayose kan badakalar N6.9bn.
Tun farko, hukumar EFCC ta gurfanar da Fayose a gaban kotu a watan Yulin 2019 kan tuhume-tuhume har guda 11.
Yadda EFCC ta gano badakalar Sambo Dasuki
Har ila yau, tun farkon shari'ar, tsohon Ministan tsaro, Musiliu Obanikoro ya fadawa kotun cewa Dasuki ya umarce shi da ya tura kudin har N1.2bn.
Obanikoro ya ce an umarce shi ya tura kudin ne daga asusun tallafi na musamman na Boko Haram.
Madaki ya ce ba kamar yadda Fayose ya yi ikirari ba cewa kudin kamfen PDP ne, an gano daga cikin kudin makamai suke a mulkin Goodluck Jonathan.
Fayose ya tona asirin basukan Buhari
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya soki yadda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi mulkin kasar.
Fayose ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi inda ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da lalata tattalin arzikin kasar.
Tsohon gwamnan na jihar Ekiti yana ganin tsohon shugaban Najeriyan ya jawowa Najeriya ci-bayan tsawon shekaru 50 a mulkinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng