An Samu Asarar Rayuka a Rikicin Manoma da Makiyaya a Jigawa

An Samu Asarar Rayuka a Rikicin Manoma da Makiyaya a Jigawa

  • An samu asarar rayuka a sabon faɗan da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a jihar Jigawa da ke yankin Arewa maso Gabas
  • Rikicin wanda ya auku a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ya jawo asarar rayukan mutum biyu yayin da aka raunata wasu mutum uku
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce an kuma lalata gonaki masu yawa a rikicin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Aƙalla mutum biyu sun rasa rayukansu sakamakon rikicin manoma da makiyaya a jihar Jigawa.

Lamarin ya auku ne bayan wasu baƙin makiyaya da suka taho daga jihar Katsina sun sake kunna wutar rikici tsakanin manoma da makiyaya a ƙananan hukumomi uku na jihar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 4 a wani hari a jihar Katsina

An yi fadan makiyaya da manoma a Jigawa
Mutum biyu sun mutum a fadan makiyaya da manoma a Jigawa Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Rikicin manoma da makiyaya ya ɓarke a Jigawa

Faɗan ya fara ne a ranar 26 ga watan Yuni a ƙauyukan Kalai, Waza, Baranda da Katanga a ƙananan hukumomin Dutse, Kiyawa da Birnin Kudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sabon faɗan na ranar Talata a ƙauyen Gauraki na ƙaramar hukumar Birnin Kudu, ƴan sanda sun ce an hallaka mutum biyu tare da raunata wasu mutum uku, cewar rahoton jaridar Premium Times.

An kuma lalata gonaki masu yawa sakamakon ɓarkewar rikicin, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Me ƴan sandan Jigawa suka ce kan rikicin?

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, Lawan Shiisu Adam, ya ce faɗan ya auku ne sakamakon gayyato makiyayan da aka yi daga jihar Katsina.

Ya bayyana cewa an hango makiyayan suna wucewa zuwa ƙauyukan Safa da Gauraki a ƙaramar hukumar Birnin Kudu, inda suka riƙa lalata gonaki wanda hakan ya sanya rikici ya ɓarke a tsakaninsu da manoma.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan mutum 116 sun rasu a wurin taron addini

"Yayin da makiyayan suke wucewa da shanunsu, mutum biyu sun rasu, ɗaya daga kowane ɓangare. An ƙona gidajen makiyaya uku."
"An gano shanun baƙin makiyayan guda 15 tare da cafke makiyaya biyar da ake zargi da gayyato baƙin makiyayan."

- Lawan Shiisu Adam

Rikicin manoma da makiyaya ya jawo asarar rayuka

A wani labarin kuma, kun ji cewa rikicin manoma da makiyaya a jihar Jigawa ya jawo asarar rayukan mutane uku a yankin gandun dajin Baranda da ke ƙaramar hukumar Kiyawa.

Rikicin ya auku ne bayan an samu saɓanin fahimta tsakanin makiyaya da manoma a yankin kan saboda furucin gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel