"Muna Tsoron Faruwar Irin Zanga Zanga Kenya": Jigon APC Ya Gargadi Tinubu
- Yayin da aka gudanar da mummunar zanga-zanga a Kenya, wani jigo a jam'iyyar APC ya gargadi Shugaba Bola Tinubu a Najeriya
- Oluyemisi Ayinde wanda jigon APC ne a Lagos ya shawarci Tinubu da ya yi gaggawar daukar mataki kan halin kunci da ake ciki
- Ayinde ya ce tabbas ana hasashen abin da ya faru a Kenya zai iya shiga sauran ƙasashen Afirka inda ya bukaci shawo kan lamarin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Jigon jam'iyyar APC a jihar Lagos, Oluyemisi Ayinde ya gargadi Bola Tinubu kan halin da ake ciki.
Ayinde ya ce akwai matsala idan har shugaban bai dauki matakin kawo karshen halin kunci da ake ciki ba a yanzu.
Halin kunci: Jigon APC ya gargadi Tinubu
Jigon APC ya fadi haka ne a cikin wata budaddiyar wasikar ga Tinubu inda ya ce suna tsoron afkuwar abin da ya faru a kasar Kenya ya faru a Najeriya, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba a manta ba, mummunar zanga-zanga ta barke na tsawon kwanaki a Kenya bayan Majalisa ta amince ta kara kudin haraji a ƙasar.
Daga bisani, shugaban kasar, William Ruto ya ki sanya hannun a kudirin bayan rasa rayuka da dama da asarar dukiyoyi sanadin zanga-zangar.
Jagoran na APC ya ba Tinubu shawara
"Mai girma shugaban kasa, abubuwa sun dagule komai sai kara tabarbarewa ya ke yi, muna tsoron barkewar zanga-zanga wanda tabbas zai jawo matsala a kasa."
"Asarar dukiyoyi da rayuka da jawo cikas ga tattalin arziki sanadin zanga-zangar zai mayar da Najeriya baya."
"Yanzu ne lokacin da ya dace ka dauki matakai domin dakile faruwar wannan matsala da ke tunkarowa."
- Oluyemisi Ayinde
Ayinde ya shawarci Tinubu da ya kafa kwamitin siyarwa da raba abinci ga ƴan ƙasa domin gudun matsalar da ke tunkarowa.
Shettima ya roki ƴan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya roki ƴan Najeriya su ci gaba goyon bayan Bola Tinubu.
Shettima ya ce Tinubu ya himmatu wurin tabbatar da inganta Najeriya da ƴan kasar domin samun walwala da kwanciyar hankali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng