Gwamnatin Ta Ba Ma’aikatu da Hukumomi Umurnin Sayen Kayan da Aka Kera a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta yi umurni ga dukkan ma'aikatu da hukumomi su tabbatar suna saye da aiki da kayayyakin da aka ƙera a gida
- Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya tabbatar da haka jiya Talata a fadar shugaban kasa yayin wani taro
- Kashim Shettima ya ce kayan da aka ƙera a gida Najeriya ba su cika samun karɓuwa ba amma lokaci ya yi da za a tabbatar da yin gyara
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta umurci ma'aikatu da hukumomi kan cigaba da amfani da kayan da aka ƙera a Najeriya.
Sanata Kashim Shettima ne ya tabbatar da haka a taron masu haɗa kayayyakin amfanin yau da kullum a Najeriya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an buɗe taron ne a jiya Talata a fadar shugaban kasa kuma za a yi kwana uku ana yinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta ce a sayi kayan Najeriya
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya yi umurni ga ma'aikatun gwamnati kan saye da amfani da kayan da aka haɗa a Najeriya.
Kashim Shettima ya ce dama akwai dokar da ta wajabata hakan a Najeriya kuma za ta cigaba da aiki har gobe.
Amfanin sayen kayan gida Najeriya
Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa sayan kayan da ka ƙera a Najeriya zai bunkasa tattalin arzikin ƙasar, rahoton TVC.
Saboda haka ya ce yan Najeriya ba su da wani uzuri na cigaba da sayen kayan da ake haɗa irinsa a Najeriya daga ƙasashen ketare.
Babbar matsalar Najeriya a yau
Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa bayyana cewa babbar matsalar Najeriya a yanzu ita ce dogaro da kashen waje.
A karkashin haka Shettima ya ce dole a cigaba da sayen kayan gida domin ganin an magance matsalar da habaka tattali.
Shettima ya bukaci ayi adalci ga Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya roki 'yan Najeriya kan mulkin Shugaba Bola Tinubu.
Shettima ya bukaci 'yan kasar su yi adalci wurin kimanta mulkin Bola Tinubu yayin da yake kokarin inganta tattalin arzikin kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng