Hankula Sun Tashi Bayan Jami'in Hukumar EFCC Ya Salwantar da Ransa

Hankula Sun Tashi Bayan Jami'in Hukumar EFCC Ya Salwantar da Ransa

  • Wani jami'in hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ya yanke wata gurguwar shawara mara daɗin ji a Abuja
  • Jami'in wanda ba a bayyana sunansa ba ya kashe kansa a cikin gidansa da ke birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 1 ga watan Yulin 2024
  • Kakakin hukumar EFCC wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani jami’in hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ya yanke shawarar barin duniya.

Jami'in na hukumar EFCC ya salwantar da ransa ne a gidansa da ke birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fadi dalilin yin doka domin rage ikon Sarkin Musulmi

Jami'in EFCC ya mutu a Abuja
Jami'in EFCC ya kashe kansa a Abuja Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ce marigayin wanda ba a bayyana sunansa ba ya kasance mamba na kwas 5 a kwalejin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin hukumar EFCC a kan lamarin

Da yake magana kan lamarin, kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana cewa ana gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.

Ya ƙara da cewa hukumar na binciko wasu abubuwan da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da ƙalubalen iyali da ka iya sanyawa jami'in ya yanke shawarar barin duniya.

Dele Oyewale ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko bayyana sunan jami’in ba har sai an kammala binciken da ake gudanarwa.

Sai dai, wasu majiyoyi daga hukumar sun shaidawa jaridar PM News cewa jami’in ya daɗe yana samun samun matsala da wata mace da shugabarsa ce a wajen aiki.

Kara karanta wannan

NYSC: Gwamna ya ba kowane 'dan bautar kasa kyautar N200,000, ya dauki matasa aiki

An umarci a cafke jami'an hukumar EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar EFCC ya ba da umarnin a kama wasu jami'ai da suka kai samame ɗakunan wani otel a jihar Legas.

Mista Ola Olukoyede ya ba da umarnin cafke jami'an ne bayan an gansu a bidiyo suna cin zarafin wata ma'aikaciyar otel din da suka kai samamen.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel