Gidan Tsohon Gwamna, Okorocha Ya Ruguje, Katafaren Gini Ya Danne Mutane a Abuja

Gidan Tsohon Gwamna, Okorocha Ya Ruguje, Katafaren Gini Ya Danne Mutane a Abuja

  • Da yammacin Talata ne gidan tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya ruguje wanda ya jefa mazauna kusa da gidan cikin zullumi
  • Rahotanni sun je ana tsaka da gyaran gidan mai hawa biyar a lokacin da ya fadi, kuma ya danne mutane da dama a birnin Abuja
  • Rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja ta tabbatar da lamarin, inda ta gaggauta gewaye gida kuma har an ceto mutane uku

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Mazauna babban birnin tarayya Abuja sun shiga zullumi lokacin da gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okoracha ya ruguje.

Gidan mai hawa biyar na yankin titin Ahmadu Bello da ke birnin tarayya Abuja, kuma ya rikito ne da misalin 9.00pm.

Kara karanta wannan

Ana gyara gini ya ruguzowa Bayin Allah a Abuja, mutane sun samu raunuka

Rochas Okorocha
Gidan tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya ruguje ana tsaka da gyara Hoto: Senator Rochas Okorocha
Asali: Facebook

The Nation ta wallafa cewa ana gyaran gidan lokacin da lamarin ya afku, kuma tuni 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja suka killace yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu mutuwa a faduwar ginin?

Nairaland ta wallafa cewa ana fargabar baraguzan gidan tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya danne mutane da dama.

Gidan ya fadi ne a yammacin Talata ana cikin gyaransa, lamarin da ya sa mutane su ka shiga cikin firgici.

Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar babban birnin tarayya, Josephine Adeh, ta tabbatar da lamarin, inda ta ce an ceto mutane uku da ransu.

Rahotanni sun bayyana cewa an kai wadanda iftila'in ya rutsa da su asibiti inda su ke karbar magani, amma ba a bayyana ko an samu mutuwa ba.

Yadda wani gini ya rikito a Kano

A wani labarin dabam, an ji cewa an shiga rudani a Kano bayan wani gini ya rikito kan jama'a a Kuntau, inda ya danne mutane da dama.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mutane sun mutu yayin da ginin katafaren Otal ya rufta a Abuja

An samu damar ceto wasu mutane biyu, amma ana fargabar akwai sauran mutane 11 da ake fargbar suna karkashin kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel