Kotu Za Ta Rataye ’Yan Bindigan da Suka Kashe Bafullatani Bayan Karbar Kudin Fansa

Kotu Za Ta Rataye ’Yan Bindigan da Suka Kashe Bafullatani Bayan Karbar Kudin Fansa

  • Babbar kotun jihar Osun ta yanke hukunci mai tsauri kan wasu yan bindiga su biyar bayan kashe wanda suka yi garkuwa da shi
  • Yan bindigar sun kashe Alhaji Ibrahim Adamu duk da cewa iyalansa sun biya kudin fansa mai yawa bayan sun yi garkuwa da shi
  • Mai shari'a Kudirat Akano ta tabbatar da cewa ta kama yan bindigar da laifuffuka hudu wanda suka saɓa dokar Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Osun - Babbar kotun jihar Osun ta yanke hukunci mai tsauri ga wasu masu garkuwa da mutane su biyar.

Rahotanni sun nuna cewa kotun ta tabbatar da cewa yan bindigar sun aikata laifuffukan da aka zarge su.

Kara karanta wannan

Kishin ƙishin din kara kudin fetur ya jawo kulle gidajen mai, jama'a sun shiga tasko

Kotu Sharia
Kotu za ta rataye 'yan bindiga. Hoto: Hoto: Witthaya Prasongsin
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mai Shari'a Kudirat Akano ce ta yankewa yan bindigar hukunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a rataye 'yan bindiga a Osun

Mai shari'a Kudirat Akano ta yanke hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane su biyar bayan kama su da laifi, rahoton Punch.

Kudirat Akano ta hukunta cewa za a kashe masu garkuwa da mutanen ne ta hanyar rataya bisa manyan laifuffuka da suka aikata.

Laifin da yan bindigar suka aikata

Babbar kotun jihar Osun ta tabbatar da cewa yan bindigar sun aikata laifuffuka hudu ciki har da garkuwa da mutane da kisan kai.

Yan bindigar sun yi garkuwa da wani Bafullatani, Alhaji Ibrahim Adamu a shekarar 2018 kuma suka kashe shi bayan sun karbi kudin fansa N3m.

Lauyan yan bindiga ya koka

Sai dai lauyan yan bindigar, Barista Bola Ige ya nuna rashin amincewa kan hukuncin da kotun ta yanke.

Kara karanta wannan

An yi musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindiga a Abuja, an kubutar da rayuka

Barista Bola Ige ya ce har a lokacin da kotun ta yanke hukuncin ba a samu dalili da ya nuna cewa lallai sun aikata laifin ba.

Za a rataye barayi a Ekiti

A wani rahoton, kun ji cewa wata kotu a jihar Ekiti ta yankewa masu fashi da makami da satar waya hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Rahoto ya nuna cewa alkallin kotun mai shari'a Blessing Ajireye ta ce an yanke musu hukuncin ne bayan an kama su da laifi dumu dumu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel