Gwamnan Kano Ya Yi Abin a Yaba, Ya Je Ta’aziyyar Kwamandan Ƴan Banga da Aka Kashe

Gwamnan Kano Ya Yi Abin a Yaba, Ya Je Ta’aziyyar Kwamandan Ƴan Banga da Aka Kashe

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gudanar da ziyarar ta'aziyya ga iyalan wani kwamandan 'yan banga da aka kashe
  • Gwamna Abba Yusuf ya kuma kai ziyarar ta'aziyya ga wasu iyalai guda biyu a wurare daban daban na cikin kwaryar Kano a makon nan
  • Mai girma gwamnan ya yi addu'ar Allah ya jikan mamatan tare da yi masu rahama kamar yadda ya fitar da sanarwa a ranar Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake yin wani abin a zo a gani yayin da ya taka da kansa har gidan wani kwamandan 'yan banga da 'yan ta'adda suka kashe.

Mai girma Abba Yusuf ya ziyarci iyalan dan bangar a rukunin gidajen Soron Dinki da ke birnin Kano domin yin ta'aziyyar mamacin.

Kara karanta wannan

Uwargidar mataimakin gwamnan Niger, Hajiya Zainab ta riga mu gidan gaskiya

Gwamnan Kano ya kai ziyarar ta'aziyya gidan kwamandan 'yan banga da aka kashe
Gwamna Abba ya je ta'aziyya gidan kwamandan 'yan banga da aka kashe a Kano. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Gwamnan da kansa ne ya wallafa batun ziyarar tare da dora hotuna a shafinsa na X a daren ranar Talata, 2 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya je ta'aziyyar kwamandan 'yan banga

A cewar Abba Yusuf:

"A jiya ne na je unguwar Soron Dinki da ke cikin birnin Kano domin jajantawa iyalan wani kwamandan ‘yan banga da wasu ‘yan ta’adda suka kashe kwanan nan.
Mun wuce zuwa rukunin gidajen Alfindiki, domin sake yin wata ziyarar ta'aziyya ga iyalan Hajiya Aishatu Nasidi."

Gwamna Abba ya yi addu'a ga mamatan

Gwamna Abba ya kuma ce sun karkare ziyarar ta'ziyyar ne da gidan Injiniya Khalil da ke rukunin gidajen Sharada, duk a cikin kwaryar Kano.

Ya yi addu'ar Allah ya jikan mamatan tare da yin rahama a gare su.

Ziyarar gwamnan na zuwa ne jim kadan bayan ganawarsa da masu aikin kwangilar gina tituna a kananan hukumomi 44 na jihar a gidan gwamnatin Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Har yanzu Ganduje bai tsira ba, Abba ya taso shi gaba a wata sabuwar badakala

Kalli hotunan ziyarar da gwamnan ya wallafa a kasa:

Matar mataimakin gwamna ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah SWT ya yiwa uwar gidan mataimakin gwamnan jihar Neja, Hajiya Zainab Garba Tukur rasuwa a ranar Talata.

Gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago ne ya bayyana hakan a ranar Talata inda ya yiwa marigayiyar addu'a da kuma ba mataimakin nasa hakurin jure wannan rashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel