Tinubu ya ziyarci Buni domin yi masa ta'aziyar rasuwar Hajiya Fatima Yuram

Tinubu ya ziyarci Buni domin yi masa ta'aziyar rasuwar Hajiya Fatima Yuram

- Bola Ahmed Tinubu, jagorar jam'iyyar APC na kasa, ya yi wa Gwamna Mai Mala Buni ta'aziyar rasuwar kakansa

- Tinubu ya ziyarci shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC ne a gidansa da ke birnin tarayya Abuja don jajenta masa

- Tinubu ya yi addu'ar Allah ya jikan Hajiya Fatima Mallum Yuram ya kuma bawa iyalanta hakurin jure rashinta

Jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a jiya Alhamis ya kai wa shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, Gwamna Mai Mala Buni ziyara.

Ya ziyarce shi ne domin yi masa ta'ziyya bisa rasuwar Hajiya Fatima Mallum Yuram, kakar gwamnan na jihar Yobe, The Nation ta ruwaito.

Tinubu ya ziyarci Buni domin yi masa ta'aziyar rasuwar Hajiya Fatima Yuram
Tinubu ya ziyarci Buni domin yi masa ta'aziyar rasuwar Hajiya Fatima Yuram. @Bunimedia
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An tsinci gawarwakin sojoji 11 da 'yan bindiga suka kaiwa hari a Benue

Hajiya Yuram ta rasu a makon da ya gabata tana da shekaru 102 a duniya kamar yadda mai magana da yawun gwamnan ya sanar.

Yayin ziyarar da Tinubu ya kai masa a gidansa da ke Wuse Zone 2 a Abuja, ya ce iyalanta za su yi kewar hikimar marigayiya Hajiya Yuram da addu'o'in ta.

Ya bayyana rasuwar marigayiyar a matsayin babban rashi ga jihar Yobe da kasa baki daya.

KU KARANTA: Jerin hamshaƙan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021 da hotunansu

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya yi addu'ar Allah ya gafarta mata ya kuma bawa iyalanta hakurin jure rashi.

Buni ya yi wa Tinubu godiya bisa lokacin da ya samu ya ziyarce shi domin yi masa ta'aziyya.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel