'Yan Bindigan da Suka Sace Mahaifiyar Rarara Sun Fadi Kudin Fansan da Za a Biya Su

'Yan Bindigan da Suka Sace Mahaifiyar Rarara Sun Fadi Kudin Fansan da Za a Biya Su

  • Ƴan bindigan da suka sace mahaifiar Dauda Adamu Kahutu sun bayyana kuɗin fansan da suke so a biya kafin su bari ta shaƙi iskar ƴanci
  • Wata majiya ta bayyana cewa ƴan bindigan sun buƙaci da a ba su N900m kafin su saki Hajiya Halima Adamu wanda ita ce ta haifi Rarara
  • Tun da farko sun nemi a ba su N1bn domin su saki dattijuwar da aka ɗauke a ƙauyen Kahutu da ke ƙaramar hukumar Danja a jihar Katsina

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ƴan bindigan da suka sace mahaifiyar shahararren mawaƙin nan Dauda Adamu wanda aka fi sani da Rarara sun faɗi kuɗin fansan da za a ba su.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan mutum 116 sun rasu a wurin taron addini

Ƴan bindigan sun buƙaci da a biya su N900m a matsayin kuɗin fansa kafin su sako Hajiya Halima Adamu wacce suka sace a Kahutu.

'Yan bindiga sun bukaci kudin fansa kan mahaifiyar Rarara
'Yan sun bukaci a ba su N900m kafin su sako mahaifiyar Rarara Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Asali: Facebook

Wata majiya da ke kusa da iyalan a Kahutu wacce ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana hakan ga jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahaifiyar Rarara: Nawa ƴan bindiga suka nema?

Majiyar ta bayyana cewa tun da farko ƴan bindigan da suka sace mahaifiyar Rarara sun kira waya inda suka buƙaci a biya su N1bn a matsayin kuɗin fansa.

"Sun kira ƴan uwanta da wayar da suka amsa a hannun ɗaya daga cikin matan da ke gidan lokacin da suka zo ɗaukar Hajiya."
"Sun buƙaci a ba su N1bn amma bayan sun ɗan yi ƴar gajeruwar tattaunawa da wani daga cikin ƴan uwanta, sun rage kuɗin zuwa N900m."
"Tun da farko sun so ne su yi cinikin da Rarara da kan shi, sai dai ya faɗa rashin lafiya tun bayan da aka ɗauke masa mahaifiya. Sun amince za su yi cinikin da wani daga cikin iyalanta."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi nasarar dakile harin 'yan bindiga sun ceto mutum 10

"Sun ba iyalanta tabbacin cewa Hajiya tana cikin ƙoshin lafiya sannan za a sake ta da zarar an biya kuɗaɗen."

- Wata majiya

An kama mutane kan sace mahaifiyar Rarara

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta cafke mutum biyu da ake zargin su da hannu a sace mahaifiyar Dauda Adamu Kahutu Rarara.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Jumu'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel