Dangote Ya Ci Gyaran Gwamnatin Tinubu, Ya Ce CBN Ya Kawo Tsarin Ruguza Sana’o’i

Dangote Ya Ci Gyaran Gwamnatin Tinubu, Ya Ce CBN Ya Kawo Tsarin Ruguza Sana’o’i

  • Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce akwai gyara a kan yadda babban bankin Najeriya ya kara kudin ruwa
  • Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa tsarin bai dace da kasa kamar Najeriya da ake kokarin samar da ayyukan yi ga al'umma ba
  • Legit ta tattauna da malamin addinin musulunci, Muhammad Abubakar kan jin yadda lamarin kudin ruwa yake a mahangar addini

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Alhaji Aliko Dangote ya ja hankalin gwamnatin shugaba Bola Tinubu kan kara kudin ruwa da CBN ya yi zuwa kashi 30%.

Aliko Dangote ya ce yin hakan zai kara durkusa sana'o'i tare da rufe kofa ga waɗanda suke ƙoƙarin fara sana'a.

Kara karanta wannan

NIN: Majalisar dattawa na kokarin kawo dokar da za ta shafi yan ƙasashen waje

Aliko Dangote
Dangote ya yi magana kan karin kudin ruwa. Hoto: Dangote Foundation
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Dangote ya yi bayanin ne a yau Talata yayin taron kungiyar MAN a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote a kan karin kudin ruwa ga sana'o'i

Alhaji Aliko Dangote ya ce karin kudin ruwa ga masu karbar rance zai hana yan kasuwa da dama zama da kafafunsu.

Dangote ya kara da cewa ba lallai a iya samar da sana'o'i da matasa ba matukar kudin ruwa ya karu sosai, rahoton Channels Television.

Har ila yau, attajirin ya ce hatta kamfanoni ba za su tsira daga shiga cikin matsalar durƙushewa ba idan aka samu karin kudin ruwa ya yi yawa.

Aliko Dangote ya bukaci gwamnati ta sassauta

Aliko Dangote ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sassauta kuɗin ruwan domin ceto sana'o'i daga rushewa.

Ya ce ya kamata gwamnatin Tinubu ta dubi yadda ƙasashen yamma suka kawo tsare-tsaren da za su tallafawa kananan sana'o'i da kamfanoni.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta yiwa wasu 'yan Najeriya gata, an dakatar da karbar haraji daga garesu

Dangote: 'Mu nisanci shigo da kayan waje'

Aliko Dangote ya yi kira ga yan Najeriya kan rage shigo da kayan amfanin yau da kullum daga ƙasashen ketare.

Ya ce hakan tamkar mutane na gayyato talauci ga kansu ne domin suna gina wasu ƙasashe maimakon gina kasarsu.

Legit ta tattauna da malamin addini

Wani malamin addini, Muhammad Abubakar ya zantawa Legit cewa dama a bangaren addini kudin ruwa ba abin da yake karawa sai wahala a kasa.

Malamin ya ce kamata ya yi idan ana son kawo sauki a kasa a cire kudin ruwa gaba daya ba ma a rage shi ba.

Motoci: Dangote zai dawo aiki da gas

A wani rahoton, kun ji cewa a kokarinsa na taimakawa Bola Tinubu wurin rage dogaro da man fetur, Aliko Dangote zai koma motoci masu amfani da gas.

Dangote ya sanar da cewa zuwa shekarar 2025, dukkan motocinsa da ke kamfanin siminti za su koma amfani da gas madadin dizil da fetur.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel