Majalisa Za Ta Binciki Zargin Yadda Ma'aikatu Suka Barnatar da N2trn a Shekara 8

Majalisa Za Ta Binciki Zargin Yadda Ma'aikatu Suka Barnatar da N2trn a Shekara 8

  • Majalisar wakilai za ta fara bincike kan yadda ma'aikatu da hukumomin gwamnati su ka kashe kudin tallafin noma da aka ba su
  • Wannan na zuwa ne saboda rashin abinci mai gina jiki da ake fama da shi a Najeriya, lamarin da majalisar ke ganin bai kamata ba
  • A kudirin da ya gabatar gaban majalisa, Hon. Chike Okafor ya ce da sake, kila ba a amfani da tallafin noma yadda ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Majalisar wakilai ta umarci kwamitinta na cimaka, samar da abinci, harkokin noma, kwalejojin noma da cibiyoyin noma da na kudi, kan wani muhimmin aiki.

Kara karanta wannan

"Kar a bari rashin tsaro ya kara kamari a Arewa," Atiku Abubakar

Majalisar na bukatar kwamitin ya gudanar da cikakken bincike kan zargin kin amfani da kudaden tallafin noma a hukumomi da ma’aikatu da gwamnati ta bayar.

Majalisa
Majalisa za ta yi bincike kan tallafin noma da gwamnati ta bayar Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta tattaro za a gudanar da bincike kan karkatar da Naira Tiriliyan 2 da gwamnati ta raba ga ma'aikatu da hukumomi cikin shekaru takwas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya biyo bayan kudiri da dan majalisa, Chike Okafor ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talata a Abuja.

''Akwai karuwar rashin abinci,'' Okafor

Yayin gabatar da kudirin, Okafor yayi nuni da cewa akwai karuwar rashin abinci da rashin abinci mai gina jiki a Najeriya.

Mista Okafor ya ce haka na faruwa sakamakon zargin almubazzaranci da kudade da aka ware domin bunkasa fannin noma a kasar.

Ya kara da cewa daga cikin shirye-shiryen da gwamnati ta samar domin tallafawa fannin noma, ta kashe sama da N2tr.

Kara karanta wannan

Jihohin Arewa 3 da aka samu sabani tsakanin sababbin gwamnoni da sarakunan gargajiya

Sai dai sakamakon almubazzaranci da kudin da sanya su a inda bai dace ba, al’ummar Najeriya na ci gaba da fama da yunwa da karancin abinci.

Kwankwaso ya rubuta wasika ga yan majalisa

A wani labarin kun ji an zargi jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso da rubuta wasika ga 'yan majalisar NNPP da ke majalisar kasar nan kan rikicin masarautar Kano.

Kungiyar Progressive League of Youth Voters ta yi zargin Kwankwaso ya shaidawa yan majalisar yadda za su caccaki shugaban kasa saboda shiga rikicin masarauta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel