NIN: Majalisar Dattawa Na Kokarin Kawo Dokar da Za Ta Shafi Yan Ƙasashen Waje
- Majalisar dattawan Najeriya na kokarin kawo dokar da za ta ba yan kasashen waje damar mallakar katin shaidar zama ɗan kasa
- An ruwaito cewa a yau Talata ne majalisar ta yi karatu na biyu ga kudurin wanda Sanata Barau Jibrin daga Kano ta Arewa ya kawo
- Yan majalisar dattawan Najeriyan sun tattauna sosai kan kudurin inda da wasu daga cikinsu suka bayyana fa'idar gabatar da shi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta yi karatu na biyu ga kudurin ba yan kasashen waje damar mallakar katin shaidar zama ɗan kasa (NIN).
A yau Talata, 2 ga watan Yuli ne majalisar ta yi karatu na biyu ga kudirin kamar yadda Legit ta tatttaro.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mataimakin shugaban majalisar, Sanata Barau Jibrin ne ya gabatar da kudirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NIN: Amfanin shigar da 'yan kasar waje
Yayin tattaunawa kan kudurin, Sanata Cyril Fasuyi ya ce shigar da yan ƙasashen waje tsarin zai faɗaɗa harkar NIN ya zamo ya shafi duniya baki daya.
Sanata Cryril Fasuyi ya ce hakan zai sa hukumar NIMC ta kara ƙaimi wajen kiyayewa da adana bayanan al'umma, rahoton Business Day.
Yan majalisar sun tattauna a kan kudirin sosai kafin daga baya sun tabbatar da shi a karo na biyu a gaban majalisar.
Za a kulle layin da ba shi da NIN
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin rufe layukan mutanen da basu lika layukansu da lambobin shaidar kasa ta NIN ba.
Wannan lamari ya zo da damuwa, kasancewar 'yan Najeriya da dama, musamman mutanen karkakara basu da lambobin NIN balle su lika da layukansu.
NIN: Kotu ta hana rufe layuka
A wani rahoton, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta haramtawa kamfanonin sadarwa na Airtel, MTN da sauransu rufe layukan mutane.
Dan rajin kare hakkin dan adam, Olukoya Ogungbeje ne ya yi karar gwamnati, babban lauyan tarayya da kuma ministan shari’a, MTN da Airtel.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng